Genesis 46

Genesis 46:1

Menene Isra'ila yayi a Biyasheba?

Isra'ila ya miƙa hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.

Wane alkawari ne Allah yayi wa Isra'ila a Biyasheba?

Allah yayi wa Isra'ila alkawari cewa zai maida shi babbar al'umma, zai sake hawro da Isra'ila kuma Yosef zai rufe idanunshi da hannunsa.

Genesis 46:5

Wanene ya tafi Masar tare da Isra'ila?

Isra'ila da dukkan zuriyarsa suka tafi Masar.

Genesis 46:12

Wane 'ya'yan Yahuda biyu ne suka mutu a ƙasar Kan'ana?

Er da Onan sun mutu a ƙasar Kan'ana.

Genesis 46:26

Mutane nawa ne na gidan Yakubu suka zo Masar?

Yawan iyalin Yakubu da suka tafi Masar su saba'in ne.

Genesis 46:28

Menene Yosef yayi domin ya sadu da mahaifinsa?

Yosef ya shirya karusarsa ya kuma tafi domin ya sami Isra'ila mahaifinsa a Goshen.

Menene Yosef ya yi sa'adda ya gan mahaifinsa?

Yosef ya rungumi wuyan mahaifinsa, ya kuma yi kuka na dogon lokaci bisa wuyansa.

Genesis 46:33

Menene Yosef ya ce wa 'yan'uwansa su faɗa wa Fir'auna game da sana'arsu?

'Yan'uwan zasu ce wa Fir'auna cewa su masu kiwon dabbobi ne tun daga ƙuruciyarsu.