Genesis 45

Genesis 45:1

Menene Yosef yayi sa'adda ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa, wanda Masarawan suka ji?

Yosef ya yi kuka da ƙarfi sa'adda ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa.

Yaya ne 'yan'uwan suka yi a lokacin da Yosef ya bayyana kansa ga garesu?

Yan'uwansa ba su iya amsa masa ba, domin sun gigice a gabansa.

Genesis 45:7

Bisa ga Yosef, don menene Allah ya aike Yosef zuwa Masar?

Allah ya aiko shi domin ya adana rai, ya kuma ajiye su da rai ta wurin babbar kuɓutarwa.

Menene Allah ya mayar da Yosef a ƙasar Masar?

Allah ya maida Yosef uba ga Fir'auna, shugaban dukkan gidansa, kuma mai mulki a cikin dukkan ƙasar Masar.

Genesis 45:9

Yaya ne Yosef ya shirya zai kulla da iyalinsa?

Yosef ya ce wa iyalinsa su zo su zauna a ƙasar Goshen inda zai tanada masu.

Genesis 45:12

Menene Yosef ya faɗa wa 'yan'uwansa su yi hanzarin yi?

Yosef ya ce ma 'yan'uwansa su yi hanzari su kawo mahaifinsa Masar.

Genesis 45:16

Yaya ne Fir'auna yayi sa'adda a ya ji cewa 'yan'uwan Yosef sun zo Masar?

Abin ya gamshi Fir'auna da bayinsa sosai, ya kuma ce wa Yosef, ya ce wa 'yan'uwansa, su ɗauko mahaifinsu da gidansu dukka su kuma zo su zauna a ƙasar Masar.

Genesis 45:21

Wanene ya ƙarbi

Benyamin ya ƙarba azurfa ɗari uku da canjin tufafi biyar, jakuna ashirin ɗauke da hatsi.

Genesis 45:24

Yaya ne Isra'ila yayi sa'adda ya ji cewa Yosef na da rai kuma shine shugaban dukka ƙasar Masar?

Zuciyarsa ta yi mamaki, domin bai gaskata da abin da suka faɗa masa ba.

Genesis 45:27

Menene Isra'ila ya faɗa cewa ya na so yayi kafin ya mutu?

Isra'ila ya ce, yana so ya gan ɗan shi kafin ya mutu.