Genesis 42

Genesis 42:1

Wanene Yakubu ya aika sayan hatsi a Masar?

'Yan'uwan Yosef guda goma, suka tafi sayan hatsi a Masar ba tare da Benyamin ba.

Genesis 42:5

Menene 'yan'uwanen Yosef suka yi sa'adda sun zo wurin Yosef sayan hatsi?

'Yan'uwanen Yosef sun rusuna masa da fuskokinsu ƙasa.

Genesis 42:7

Menene Yosef yayi sa'adda ya gane 'yan'uwan shi?

Yosef ya ɓadda kamarsa ya kuma yi wa 'yan'uwansa magana da zafi.

Genesis 42:9

Wane zargi neYosef yayi akan 'yan'uwansa?

Yosef yayi zargin 'yan'uwansa cewa sun zama 'yan leƙen asirin ƙasa.

Genesis 42:12

Ina ne 'yan'uwan Yosef suka ce ƙaraminsu yake?

'Yan'uwan Yosef sun ce ƙaraminsu ya na tare da mahaifinsa a ƙasar Kan'ana.

Ina ne 'yan'uwan Yosef suka ce ɗayan ɗan'uwansu yake?

'Yan'uwan Yosef sun ce ɗayan ɗan'uwan baya da rai.

Genesis 42:14

Wane gwaji ne Yosef yayi wa 'yan'uwansa domin su nuna cewa su ba 'yan leƙen asirin ƙasa ba ne?

Yosef ya faaɗ cewa 'yan'uwansa ba zasu bar Masar ba sai ƙaramin ḍan'uwansu ya zo Masar.

Ina ne Yosef ya sa 'yan'uwansa har zuwa wane tsawon lokaci?

Yosef ya sa aka dukkan kulle su har kwana uku.

Genesis 42:18

Menene Yosef ya ce wa 'yan'uwansa su yi domin su rayu?

Yosef ya ce masu su bar ɗaya daga cikin 'yan'uwansu a tsare shi a kurkuku, sa'adda sauran su kai hatsi Ƙana'na su kuma kawo ƙaramin ɗan'uwansa.

Genesis 42:21

Don menene 'yan'uwan Yosef suka gaskanta cewa wannan damuwan ya zo masu?

Sun gaskanta cewa ana neman jinin Yosef domin abinda sun yi.

Genesis 42:23

Menene Yosef yayi sa'adda ya ji 'yan'uwansa suna magana game da abinda suka yi masa?

Sa'adda Yosef ya ji 'yan'uwansa suna magana game da abinda suka yi masa, ya juya daga gare su ya yi kuka.

Menene Yosef ya sa aka maida wa kowa cikin bahunsa?

Yosef ya sa wa 'yan'uwansa kuɗinsa a cikin bahunsa.

Genesis 42:26

Ya ya ne 'yan'uwan sun yi a lokacin da ji cewa buhun ɗaya daga cikinsu na da kuɗinsa a ciki?

Zukatansu suka nitse sun kuma juya suna rawar jiki ga junansu.

Wanene 'yan'uwan suka yi zargin damuwowinsu na yanzu?

Sun ba Allah laifi, suna tambayan dalilin da Allah yayi masu wannan.

Genesis 42:35

Menene 'yan'uwan da Yakubu suka gane sa'adda suka zazzage bahunansu?

Sun gane cewa kowanne mutum, jakkar azurfarsa na cikin bahunsa.

Menene Yakubu ya ji tsoro cewa zai faru domin yanayinsu?

Yakubu ya ji tsoron cewa za a ɗauke mashi Simiyon da Benyamin.

Genesis 42:37

Wane alkawari ne Ruben yayi wa Yakubu?

Ruben ya rantse cewa zai dawo wa Yakubu da Benyamin daga Masar; ko kuma a kashe 'ya'yansa.

Yakubu ya amince wa Ruben ya tafi Masar da Benyamin?

A'a, Yakubu bai yarda Ruben ya ɗauke Benyamin zuwa Masar ba.

Menene Yakubu ya faɗa cewa zai faru da shi idan Benyamin ya mutu?

Yakubu ya faɗa cewa zai yi bakinciki har zuwa lahira idan Benyamin ya mutu.