Genesis 41

Genesis 41:4

A mafarkin Fir'auna na farko, menene shanun marasa ban sha'awa ramammu suka yi wa masu ban sha'awa da ƙiba?

Shanun marasa ban sha'awa ramammu sun cinye shanun masu ban sha'awa da ƙiba.

Genesis 41:7

A mafarkin Fir'auna na farko, menene ƙananun kawunan suka yi wa kawunan cikakku masu kyau?

Ƙananun kawunan sun haɗiye kawunan cikakku masu kyau kuma.

Yaya ne 'yan dabo da masu hikima Fir'auna suka fasara mafarkinsa?

'Yan dabo da masu hikima basu iya fasara mafarkin Fir'auna ba.

Genesis 41:12

Menene mai riƙon ƙoƙon ya ce game da Yosef?

Mai riƙon ƙoƙon ya faɗa wa Fir'auna cewa wani saurayin mutumin Ba'ibraniye ya fasara masa mafarkinsa da kyau da kuma mafarkin wani mutum a lokacin da suke tsare.

Genesis 41:14

Wanene Yosef ya faɗa cewa zai fasara mafarkin Fir'auna?

Yosef ya faɗa cewa Allah zai amsawa Fir'auna da tagomashi

Genesis 41:25

Menene Yosef ya ce Allah zai bayyana wa Fir'auna?

Yosef ya ce Allah zai bayyana wa Fir'auna abin da yake gaf da aiwatarwa.

Menene shanun masu kyau guda bakwai da kawunan hatsin bakwai suke wakilta?

Shanun masu kyau guda bakwai suna wakilcin shekaru bakwai.

Genesis 41:27

Menene shanun bakwai ramammu marasa ban sha'awa da kawunan hatsin ƙanana suke wakilta?

Shanun bakwai ramammu marasa ban sha'awa suna wakilcin shekaru bakwai na yunwa.

Genesis 41:30

Bisa ga Yosef, don menene aka ba wa Fir'auna mafarkai biyu?

An ba wa Fir'auna mafarkai biyu domin Allah ya tabbatar da al'amarin, kuma Allah zai aiwatar ba da daɗewa ba.

Genesis 41:33

Wane murabban amfanin Masar ne Yosef ya ba wa Fir'auna shawarar su ɗauka a shekaru bakwai na yalwa?

Yosef ya ba wa Fir'auna shawarar cewa ya zaɓi shugaba ya ɗauki kashi biyar na amfanin Masar a cikin shekaru bakwai na yalwa.

Genesis 41:37

Menene Fir'auna ya faɗa ke cikin Yosef?

Fir'auna ya faɗa cewa Ruhun Allah na cikin Yosef.

Genesis 41:39

Wane sashin iko ne Fir'auna ya ba wa Yosef?

Fir'auna ya ba wa Yosef iko bisa gidansa da kuma dukka ƙasar Masar kuma shi ne na biyu ga Fir'auna.

Genesis 41:48

Menene yawan hatsin da Yosef ya tara a shekaru bakwai na yalwar?

Yosef ya ajiye hatsi kamar rairayin teku, da yawan gaske har ya daina ƙirgawa, saboda ya zarce ƙirgawa.

Genesis 41:50

Menene sunayen 'ya'yan Yosef da aka haifa kafin yunwa?

An sa wa 'ya'yan Yosef suna Manasse da Ifraimu.

Genesis 41:53

Yaya ne bazuwan yunwan a shekaru bakwan?

Aka yi yunwa a cikin dukkan ƙasashen.

Genesis 41:55

Menene Yosef yayi sa'adda mutanen Masar suka yi kuka ga Fir'auna don abinci?

Yosef ya buɗe dukkan gidajen ajiya ya sayar da abinci wa Masarawa.

Wanene suka zo Masar domin sayan abinci daga Yosef?

Dukkan duniya na zuwa Masar su sayi hatsi daga wurin Yosef.