Genesis 34

Genesis 34:1

Menene Shekem, ɗan Hamo yayi a lokacin da ya gan Dina, ɗiyar Liya?

Shekem ya kuma cafke ta, ya ɓata ta, ya kuma kwana da ita.

Genesis 34:4

Menene Yakubu ya far yi a lokacin da ya ji game da abinda ya faru da Dina?

Yakubu ya kame bakinsa har sai da suka zo.

Genesis 34:6

Menene amsar 'ya'yan Yakubu a lokacin da suka ji abinda Shekem yayi wa Dina?

'Ya'yan Yakubu sun yi fushi.

Genesis 34:8

Menene Hamo, mahaifin Shekem yake son Yakubu yayi?

Hamo ya so Yakubu ya ba Shekem Dina a matsayin matarsa, kuma su yi auratayya da su.

Genesis 34:11

Menene Shekem ya na da niyar yi don ya aure Dinah?

Shekem ya faɗa cewa zai biya duk abinda suka ce masa.

A wane hanya ne 'ya'yan Yakubu suka amsa Shekem kuma don menene?

'Ya'yan Yakubu sun amsa Shekem da zamba saboda Shekem ya ɓata Dinah 'yar'uwarsu.

Genesis 34:14

Wane sharaɗi ne 'ya'yan Yakubu suka yi wa Hamo kafin su amince auratayya da iyalinsa?

'Ya'yan Yakubu sun ba da sharadin cewa dukka mazajen iyalin Hamo su yi kaciya.

Genesis 34:22

Sa'adda suke magana da mutanen garin, menene Hamo da Shekem suka ce zai zama nasu idan suka yi auratayya da iyalin Yakubu?

Sun faɗa cewa dukka dabbobin Yakubu da kaddarorinsa za su zama nasu idan sun yi auratayya da iyalin Yakubu.

Genesis 34:24

Ya ya ne mutanen Hamo suka amsa a lokacin da kak tambayae su ko so na so a yi masu kaciya?

Mutanen Hamo sun saurare shi da Shekem kuma an yi wa kowane namiji kaciya.

Menene Simiyon da Lebi suka yi a rana ta uku bayan aka yi wa mazajen iyalin Hamo kaciya?

Simiyon da Lebi sun ƙashe dukka mazajen garin Hamo.

Genesis 34:27

Menene kuma dukka 'ya'yan Yakubu suka yi?

Dukka 'ya'yan Yakubu suka washe birnin, suka ɗauki dukka dukiyarsu, suka kuma kama dukka 'ya'yayensu da matayensu.

Genesis 34:30

Yaya ne Yakubu yayi a lokacin da ya ji game da abin da Simiyon da Lebi suka yi?

Yakubu ya faɗa cewa Simiyon da Lebi sun kawo masa matsala, domin mazaunan ƙasar na iya hallaka shi da iyalinsa.

Don menene Simiyon da Lebi suka ce sun yi?

Simiyon da Lebi sun faɗa cewa sun yi domin Shekem ya yi da 'yar'uwarsu kamar karuwa.