Genesis 33

Genesis 33:1

Sa'adda Isuwa yana zuwa wurin Yakubu, a wane shiri ne Yakubu ya sa matansa a bayanshi?

Yakubu ya fara sa mata barori, sai Liya, sai Rahila.

Menene Yakubu yayi sa'adda ya yi kusa da ɗan'uwansa?

Yakubu ya rusuna zuwa ƙasa sau bakwai, har sai da ya zo kusa da ɗan'uwansa.

Genesis 33:4

Menene Isuwa yayi a lokacin da ya zo wurin ɗan'uwansa?

Isuwa ya rugo ya same shi, ya rungume shi, ya rungumi wuyansa, ya sumbace shi kuma.

Genesis 33:9

Menene Isuwa ya gaya wa Yakubu ya yi da ƙyautar da ya aika masa?

Isuwa ya ce ma Yakubu ya bar shi wa kansa tunda ya na da isassu.

Wane dalilai biyu ne Yakubu ya ba wa Isuwa don ya ƙarbi ƙyautarsa?

Yakubu ya faɗa cewa saboda Allah ya aiwatar da alheri zuwa gare shi, saboda kuma ya na da isassu, Esuwa ya karɓi ƙyauta.

Genesis 33:12

Don menene Yakubu ya ce yana son Isuwa ya wuce gaba, sa'adda shi zai yi tafiya a hankali?

Yakubu ya ce yana son Isuwa ya wuce gaba domin dabbobin za su mutu idan an kore su da ƙarfi.

Ina ne Yakubu ya ce zai je ya kawo iyalinsa da tumakansa?

Yakubu ya ce zai je ya kawo iyalinsa da tumakansa wa Isuwa a Seyir.

Genesis 33:15

Zuwa ina ne Yakubu yayi tafiya, inda ya gina wa kansa gida?

Yakubu yayi tafiya zuwa Sukkot, inda ya gina wa kansa gida.

Genesis 33:18

Zuwa ina ne Yakubu yayi tafiya, inda ya sayi fili?

Yakubu yayi tafiya zuwa Shekem inda ya sayi fili.