Genesis 18

Genesis 18:1

Sa'adda Ibrahim ya na zaune kofan a tenti, menene ya gani a lokacin da ya duba sama?

Ibrahim ya gan mutane uku a tsaye kewaye da shi.

Genesis 18:3

Menene Ibrahim ya ba wa mutanen?

Ibrahim ya ba mutanen ɗan ruwa don su wanke ƙafafunsu da abinci.

Genesis 18:9

Ina ne Saratu take a lokacin da bãƙin su suka bada wannan annabcin?

Saratu tana cikin runfa.

Wane annabici ne bãƙin suka yi wa Saratu?

Ɗaya daga cikin bãƙin ya ce sa'adda zai komo, Saratu za ta sami ɗa.

Genesis 18:11

Yaya ne Saratu ta amsa annabcin bãƙin?

Saratu ta yi dariya da ta ji annabcin bãƙin.

Genesis 18:13

Menene Yahweh, bakon, ya ce game da amsar Saratu?

Yahweh ya tambaya dalilin da Saratu take dariya sa ya kuma ce "akwai abin da ke da wuya ne ga Yahweh?

Genesis 18:16

Sa'ada mutanen suka bar gidan Ibrahim, zuwa ta ina ne suka tafi?

Mutanen sun bar gidan Ibrahim suka tafi ta Saduma.

Wane tambaya ne Yahweh yayi sa'adda suke tafiya?

Yahweh ya ce, "in ɓoye wa Ibrahim abin da nake so in aikata"?

Menene Yahweh ya ɗole ne Ibrahim yayi domin ya cika alkawarinsa?

Yahweh ya faɗa cewa ɗole ne Ibrahim umarci 'ya'yansa da iyalinsa domin su aikata adalci da aikin adalci.

Genesis 18:20

Don menene mutanen su na zuwa ta Saduma?

Mutanen suna tafiya ta Saduma domin kuka kan Saduma da Gomara ya yi yawa kuma sun so su gani ko biranen suna da mugunta kamar yadda kukan ya nuna.

Genesis 18:22

Sa'adda Ibrahim ya tsaya da Yahweh, wane tambaya ne yayi wa Yahweh?

Ibrahim yayi tambaya cewa, "za ka share adalai tare da mugaye?

Genesis 18:24

Menene Yahweh ya ce zai yi idan akwai adalai hamsin a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.

Genesis 18:27

Menene Yahweh ya ce zai yi idan akwai adalai arba'in da biyar a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.

Genesis 18:29

Menene Yahweh ya ce zai yi idan akwai adalai arba'in a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.

Menene Yahweh ya ce zai yi idan akwai adalai talatin a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.

Menene Yahweh ya ce zai yi idan akwai adalai ashirin a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.

Genesis 18:32

Menene Yahweh ya ce zai idan akwai dalai goma a cikin garin?

Yahweh ya ce zai kuɓutar da dukkan birnin sabo da su.