Genesis 17

Genesis 17:1

Shakaru nawa Ibram yake a lokacin da Yahweh ya bayyana masa domin ya tabbatar da alkawarinsa?

Ibram ya kai shekaru tasa'in da tara a lokacin da Yahweh ya bayyana masa.

Wane umarne ne Yahweh ya ba wa Ibran game da rayuwarsa?

Yahweh ya umarce Ibrm ya yi tafiya a gabansa ya kuma zama da rashin laifi.

Genesis 17:3

Zuwa menene Yahweh ya canza sunar Ibram kuma menene sunar ke mufi?

Yahweh ya canza sunar Ibram zuwa Ibrahim wanda ke nufin "uban al'ummai masu yawa."

Genesis 17:7

Menene Yahweh ya fara ba wa zuriyar Ibrahim a matsayin alkawarin?

Yahweh ya ba wa zuriyar Ibrahim dukka ƙasar Kan'ana domin ta zama ɗaya daga cikin alkawarin.

Menene Yahweh ya faɗa cewa zai zama dangantaka sakanin zuriyar Ibrahim da Yahweh?

Ibrahim ya faɗa cewa zai zama Allah ga zuriyar Yahweh.

Genesis 17:9

Menene Yahweh ya umarta cewa a yi a matsayin alama sakanin Ibrahim da Yahweh?

Yahweh ya umarta cewa ɗole a yi wa kowane na miji kaciya don ya zama alamar alkawari sakanin Ibrahim da Yahweh.

Genesis 17:12

A wane shekara ne ake yi wa yaro kaciya?

Ana yi wa yaro kaciya bayan kwana takwas.

Menene za a yi da bãƙin da suka shiga cikin iyalin da ke cikin alkawari da Yahweh?

An yi wa bãƙin da ke cikin iyalin da aka yi alkawari da Yahweh.

Menene ya faru da duk namijin da bai yi kaciya ba?

Duk wani namiji wanda ba shi da kaciya za a fitar da shi daga cikin mutanensa domin ya karya alkawarina.

Genesis 17:15

Zuwa menene Yahweh ya canza wa Sarai sunarta?

Yahweh ya canza sunar Sarai zuwa Saratu.

Menene Yahweh yayi alkawari cewa zai fito ta wurin Saratu?

Yahweh yayi alkawari cewa ɗan Ibrahim zai fito ta wurin Saratu.

Genesis 17:17

Yaya ne Ibrahim ya amsa alkawarin Yahweh game da Saratu?

Ibrahim yayi dariya ya kuma tambaya yadda za a haifa ɗa wa mutunen da sun tsufa.

Genesis 17:19

Menene Allah ya ce ɗole Ibrahim ya sa wa sunar ɗan da zai fito daga Saratu?

Allah ya faɗa wa Ibrahim cewa ɗole ne sa wa ɗan suna Ishaku.

Menene Allah ya ce zai kafa da Ishaku?

Allah ya ce zai kafa alkawarinsa da Ishaku.

Wane alkawari ne Allah yayi game da Ishaku?

Allah yayi alkawari cewa zai ruɓanɓaya Isma'ila ya kuma wadatar da shi sosai ya kuma maishe shi babban al'umma.

Genesis 17:24

Bayan da Allah ya bar Ibrahim, menene Ibrahim yayi wannan ranar?

A wannan ranar, Ibrahim ya yi wa dukka mazajen gidansa kaciya.

Shekara nawa Isma'ila yake a lokacin da aka yi mashi kaciya?

Isma'ila yana da shekaru sha uku a lokacin da aka yi masa kaciya.