Genesis 44

Genesis 44:1

Menene Yosef ya ce ma ma'aikacin yayi da bahunan 'yan'uwansa kafin suka tafi?

Yosef ya ce ma ma'aikacin ya cika bahunan 'yan'uwansa da abinci, ya kuma maida wa kowannen su kuɗinsa cikin bakin bahunsa, ya kuma sanya kofin azurfa, cikin bakin bahun ƙaramin

Genesis 44:3

A takaice, menene Yosef ya faɗa wa ma'aikacinsa ya ce ma 'yan'uwansa sa'adda ya bi bayan mutanen, idan kuma ya sha kansu?

Yosef ya faɗa wa ma'aikacinsa cewa ya tambaye dalilin da suka maida mugunta domin nagarta ya kuma yi zargin su da sata kofin Yosef.

Genesis 44:8

Menene 'yan'uwan suka rantse cewa za su yi idan ḍaya daga cikinsu ya saci kofin Yosef?

'Yan'uwan sun faɗa cewa wanda aka same shi da kofin zai mutu kuma sauran zasu zama bayi.

Wane hukunci ne ma'aikacin ya ce zai bukaci idan an sãta kofin?

Ma'aikacin ya faɗa cewa wanda aka same shi da kofin a wurinsa zai zama bawansa, kuma sauran zasu fita daga zargi.

Genesis 44:11

Menene ma'aikacin ya samu kuma yaya ne 'yan'uwan suka yi?

Ma'aikacin ya sami kofin a bahun Benyamin kuma 'yan'uwan sun yaga tufafinsu.

Genesis 44:14

Menene 'yan'uwan suka yi sa'adda suka dawo gidan Yosef?

'Yan'uwan suka rusuna a gaban Yosef har ƙasa.

Genesis 44:16

Wanene Yahuda ya faɗa cewa ya samu laifin 'yan'uwan?

Yahuda ya ce Allah ya gãno laifinsu.

Menene Yahuza ya ce dukka 'yan'uwan zasu zama?

Yahuda ya ce dukka 'yan'uwan zasu zama bayin Yosef.

Wane hukunci ne Yosef ya ce zai yi wa 'yan'uwan?

Yosef ya faɗa cewa mutumin da aka iske kofin a hannunsa, zai zama bawansa, amma game da sauran, zasu tafi cikin salama.

Genesis 44:20

Wane dalili ne Yahuda ya bayar akan ƙaunar mahaifinsa ga ƙaramin ɗan'uwansu?

Yahuda ya faɗa cewa ƙaramin ɗan'uwansu ne ɗan tsufansa kuma shi kaɗai ne ya rage ga mahaifiyarsa.

Menene 'yan'uwan suka damu cewa zai faru da mahaifinsu idan ƙaramin ya bar shi?

'Yan'uwan sun damu cewa har ya bar mahaifinsa to mahaifinsa zai mutu.

Genesis 44:23

Don menene Yahuda ya faɗa cewa an tilasta 'yan'uwan su zo da Benyamin zuwa Masar?

Yahuda ya faɗa cewa an tilasta su su kawo Benyamin domin Yosef ya faɗa cewa sai ƙaramin ɗan'uwan ya zo kafin su gan furskansa.

Genesis 44:27

Menene Isra'ila ya yi tunani cewa ya faru da Yosef?

Isra'ila ya zata cewa an yage Yosef gutsu-gutsu.

Menene Isra'ila ya ce zai faru da shi idan an ɗauke Benyamin daga gare shi?

Isra'ila ya faɗa cewa 'yan'uwan zasu gangara da furfurasa da baƙinciki zuwa Lahira.

Genesis 44:30

Menene Yahuda ya faɗa cewa zai faru da mahaifinsu idan basu dawo da Benyamin ba?

Yahuda ya ce mahaifinsu zai mutu.

Wane tabbaci ne akan Benyamin, Yahuda ya ce ya zama?

Yahuda ya faaɗ cewa idan bai maido da Benyamin ga mahaifinsu ba, zai ɗauki laifin ga mahaifina har abada.

Genesis 44:33

Menene Yahuda ya ce wa Yosef yayi wa Benyamin domin ya koma wurin mahaifinsa?

Yahuda ya roƙe Yosef ya sa shi ya zama bawansa domin Benyamin ya iya koma wurin mahaifinsa.