Genesis 43

Genesis 43:1

Don menene Isra'ila ya faɗa wa 'ya'yansa su sake tafiya zuwa sayan abinci a Masar?

Yunwa ta yi tsanani kuma sun cinye hatsin da suka kawo daga Masar a tafiya na farko.

Genesis 43:3

Menene Yahuda ya faɗa cewa ɗole ne su samu domin su tafi Masar kuma?

Yahuda ya faɗa cewa ɗole ne su samu ɗan'uwansu Benyamin domin su tafi zuwa Masar.

Genesis 43:8

Wane alkawari ne Yahuda yayi wa mahaifinsa Isra'ila?

Yahuda ya faɗa cewa idan bai dawo da Benyamin ba, za a riƙe shi da hakkinsa.

Genesis 43:11

Menene Isra'ila ya faɗa wa 'yan'uwan su ɗauka zuwa Masar?

Isra'ila ya faɗa wa 'yan'uwan cewa su ɗauki mafi kyau daga cikin amfanin ƙasar su kuma ɗauki kuɗi ka shi biyu.

Genesis 43:13

Menene Isra'ila ya roƙe Allah game da tafiyan?

Isra'ila ya roƙe Allah ya ba 'yan'uwan jinƙai a Masar domin a saki dukka 'yan'uwan.

Genesis 43:18

Yaya ne 'yan'uwan suka amsa sa'adda aka kawo su gidan Yosef, kuma don menene?

'Yan'uwannen sun ji tsoro kila a kama su a kuma ɗaure su ya ɗauke su a matsayin bayi, saboda kuɗaɗen da a ka maido masu cikin bahunansu.

Genesis 43:21

Menene 'yan'uwan suka faɗa wa ma'aikacin gidan Yosef?

'Yan'uwan sun faɗa wa ma'aikacin cewa sun dawo da kuɗin da aka bari a cikin buhunnasu da kuma kuɗin sayan abinci.

Daga ina ne ma'aikacin ya ce kuɗin da aka bari a cikin bahunan ya fito?

Ma'aikacin ya ce kuɗin da aka bari a cikin bahunan ya fito daga Allah.

Genesis 43:26

Menene 'yan'uwan suka yi sa'adda Yosef ya zo gida?

'Yan'uwan suka kawo kyaututtukan da ke hannuwansu cikin gidan, su ka kuma rusuna a gabansa har ƙasa.

Game da wanene Yosef ya tambaye 'yan'uwansa?

Yosef ya tambaye 'yan'uwanshi game da lafiyar mahaifinsu.

Genesis 43:30

Don menene Yosef yayi saurin fita daga dakin, kuma menene yayi bayan da ya tafi?

Yosef yayi hanzari ya fita daga ɗakin saboda ya motsu sosai game da Benyamin sai ya tafi ɗakinsa yayi kuka.

Genesis 43:32

Don menene Masarawa da Ibraniyawa suke cin abinci dabam dabam?

Domin abin ƙyama ne ga Masarawa.

Yaya ne aka shirya 'yan'uwan a teburin?

An shirya 'yan'uwan a teburin bisa ga matsayin haihuwarsa.

Menene ya zama dabam game da abincin da aka ba wa 'yan'uwan?

Kason Benyamin ya yi sau biyar fiye da na 'yan'uwansa.