Genesis 40

Genesis 40:1

Don menene sarkin Masar ya sa mai riƙon ƙoƙonsa da mai toye-toyensa a kurkuku?

Ya sasu a cikin kurkuku domin sun yi mashi laifi.

Genesis 40:4

Menene ya faru da mai riƙon ƙoƙon da mai toye-toyen a ɗare ɗaya?

Mai riƙon ƙoƙon da mai toye-toyen sun yi mafarki a dare ɗaya.

Genesis 40:6

Don menene mai riƙon ƙoƙon da mai toye-toyen suke bakin ciki washegari?

Sun yi bakin ciki domin babu wanda ya iya fasara mafarkinsu.

Wanene Yosef ya faɗa cewa zai iya fasara mafarkan?

Yosef ya faɗa cewa Allah zai iya fasara mafarkan.

Genesis 40:12

Menene Yosef ya faɗa cewa shi ne fasarar mafarkin mai riƙon ƙoƙon?

Yosef ya faɗa cewa mafarkin na nufin a cikin kwanaki ukku, Fir'auna zai ɗaga shi ya kuma mai da shi wurin aikinsa.

Genesis 40:14

Wane roko ne Yosef yayi wa mai riƙon ƙoƙon bayan fasarar mafarkinsa?

Yosef ya roka cewa mai riƙon ƙoƙon ya tuna da shi, ya ambace shi wurin Fir'auna a fitar da shi daga wannan kurkuku.

Genesis 40:18

Menene Yosef ya faɗa cewa shi ne fasarar mai toye-toye?

Yosef ya faɗa cewa mafarkin na nufin a cikin kwana uku, Fir'auna zai ɗaga kan shi daga gare shi zai kuma sarƙafe shi bisa itace.

Genesis 40:20

Wane abu ne na musamman ya faru bayan kwana uku?

Rana ta uku ranar tunawa da haihuwar Fir'auna ce.

Menene Fir'auna yayi da mai riƙon ƙoƙon da mai toye-toye a wannan ranar?

Fir'auna ya maido da shugaban masu riƙon ƙoƙon amma ya sargafe mai toye-toyen kamar yadda Yosef ya fasara masu.

Mai riƙon ƙoƙon ya tuna da rakon da Yosef yayi masa?

A'a, mai riƙon ƙoƙon bai tuna da rakon da Yosef yayi masa amma ya manta da shi.