Genesis 39

Genesis 39:1

Wanene ya sayi Yosef a Masar?

Fotifa, maƙaddashin Fir'auna kuma hafsan masu tsaro na ya sayi Yosef a Masar.

Genesis 39:3

Don menene Yosef ya sami tagomashi a Masar?

Yosef ya sami tagomashi domin Yahweh yana tare da shi.

Genesis 39:5

Menene Fotifa ya sa Yosef lura?

Fotifa ya sanya kowanne abu da ya ke da shi a ƙarƙashin lurar Yosef.

Genesis 39:7

Menene matan Fotifa ta sa Yosef yayi?

Matan Fotifa ta sa Yosef ya kwana da ita.

Yaya ne Yosef ya amsa rokon matar Fotifa?

Yosef ya ya ƙi ya kwana da ita ya kuma fada cewa ba zai iya aikata wannan babban mugunta ya kuma yi zunubi wa Allah ba.

Genesis 39:10

Menene Yosef yayi a lokacin da matar Fotifa ta kama shi ta tufafinsa?

Yosef ya bar tufafinsa a hannunta, ya tsere, ya fita waje.

Genesis 39:13

Wane zargi ne matar Fotifa ta yi akan Yosef?

Ta yi zargin shi da cewa ya so ya kwana ta ita ba tare da son ta ba.

Genesis 39:19

Menene Fotifa yayi sa'adda ya ji zargin akan Yosef?

Fotifa ya fusata sosai sai ya sa Yosef a cikin kurkuku.

Genesis 39:21

A wannan lokacin, menene Yahweh ya nuna wa Yosef?

Yahweh ya nuna wa Yosef alkawarin aminci a a wannan lokacin.

Menene shugaban kurkukun ya sa a karkashin Yosef?

Shugaban kurkukun ya sa dukkan fursunonin da ke cikin kurkukun cikin hannun Yosef.

Menene sakamakon dukka abubuwan da Yosef yayi kuma don menene?

Duk abin da Yosef yayi Yahweh na wadatar da shi.