Genesis 50

Genesis 50:1

Menene Yosef yayi da jikin Isra'ila bayan mutuwarsa?

Yosef ya sa aka nannaɗe Isra'ila da maganin hana ruɓewa.

Genesis 50:4

Wane roƙo ne Yosef yayi wa Fir'auna game da bison mahaifinsa kuma don menene yayi wannan roƙon?

Yosef yayi roƙo domin ya iya zuwa ƙasar Kan'ana don ya bizne mahaifinshi kamar yadda mahaifinsa ya sa shi ratsuwa.

Genesis 50:7

Wanene ya tafi da Yosef bison Isra'ila?

Dukkan 'yan majalisar Fir'auna suka tafi tare da shi - dattawan gidansa, dukkan manyan masu gari da 'yan gidan Yosef da 'yan'uwansa, da gidan mahaifinsa, karusai da mahaya dawaki suka tafi tare da shi.

Genesis 50:10

Menene Kan'anawan sun ce sa'adda suka gan Yosef da waɗanda ke tare da shi?

Kan'anawan sun ce wannan taro ne na baƙinciki sosai ga masarawa.

Genesis 50:12

Ina ne Yosef suka tafi bayan da sun bizne mahaifinsu?

Bayan da Yosef ya bizne mahaifinsa, sai ya koma cikin ƙasar Masar, shi, tare da 'yan'uwansa.

Genesis 50:15

Game da menene 'yan'uwan Yosef suka damu bayan mutuwar Isra'ila?

'Yan'uwan Yosef sun damu cewa Yosef zai riƙe su da fushi gãba da su domin dukka muguntan da sun yi mashi.

Menene 'yan'uwan Yosef suka roƙa game da laifin da sun yi wa Yosef?

'Yan'uwan sun roƙo Yosef ya gafarta masu laifin da suka yi akan Yosef.

Genesis 50:18

Menene 'yan'uwan Yosef sun yi sa'adda suka zo wurin Yosef?

Sa'addda suka zo wurin Yosef, 'yan'uwan Yosef sun rusuna a gabansa.

Wane alheri ne Yosef ya ce Allah yayi ta wurin muguntar 'yan'uwansa?

Yosef ya ce Allah ya yi niyyar alheri domin a adana rayuwar mutane da yawa.

Genesis 50:22

Menene tsawon rayuwar Yosef?

Yosef ya yi rayuwa shekaru ɗari da goma.

Genesis 50:24

Menene Yosef ya ce ya yi kusan faruwa da shi?

Yosef ya ce yayi kusan mutuwa.

Wane alkawari ne Yosef ya ce Allah zai cika wa zuriyar Isra'ila?

Yosef ya ce Allah zai zo wa mutanen ya kuma bida su hayewa daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse zai ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

Menene Yosef ya sa mutanen Isra'ila suka rantse cewa za su yi?

Yosef ya sa su rantsuwa cewa zasu ɗauki ƙasusuwan Yosef daga Masar sa'adda sun bar Masar.

Menene ya faru da jikin Yosef bayan da ya mutu?

An nannaɗe jikin Yosef da maganin hana ruɓa kuma aka ajiye shi cikin akwati a Masar.