Genesis 38

Genesis 38:1

Daga ina ne Yahuda ya ɗauki mata?

Yahuda ya ɗauki mata daga mutum Kan'aniya.

Genesis 38:6

Menene Yahweh yayida ɗan fãri na Yahuda Er kuma don menene?

Yahweh ya kashe Er domin mugu ne.

Genesis 38:8

Yaya neOnan, ɗan Yahuda na biyu bai cika aikinsa na ɗan'uwan miji a gare ta don ya sama wa ɗan'uwansa ɗa ba?

Onan ya zubar da maniyin a ƙasa a lokacin da ya kwana da Tama.

Menene Yahweh yayi da ɗan Yahuda na biyu, kuma don menene?

Yahweh ya kashe Onan domin abinda yayi mugunta ne.

Genesis 38:11

Menene alkawarin da Yahuda yayi wa Tama?

Yahuda yayi wa Tama alkawarin ɗansa na uku a matsayin miji idan yaya girma.

Genesis 38:12

Bayan tsawon lokaci, don menene Yahuda ya na bukatar karfafawa?

Yahuda ya ta'azantu domin matarsa ta mutu.

Menene Tama ta yi sa'adda ta ji cewa Yahuda zai tafi Timna?

Tama ta tuɓe tufafin gwaurancinta kuma ta rufe jikinta da abin lulluɓi ta kuma ɗaura wa jikinta. Ta zauna a ƙofar Enayim, wadda ke kan hanyar zuwa Timna.

Don menene Tama ta yi haka?

Tama ta yi haka domin ta ga Shela ya girma amma ba a ba da ita a gare shi a matsayin mata ba.

Genesis 38:17

Menene Tama ta ƙarba a matsayin alamar kuɗin da Yahuda ya kwana da ita?

Yahuda ya ba Tama zoben hatiminsa da ɗamararsa, da sandar dake a hannunsa.

Genesis 38:21

Sa'adda Yahuda ya so ya ƙarbi abubuwansa ta wurin biyan karuwan da ɗan akuya, menene ya ji?

Yahuda ya ji cewa babu wata karuwar asiri dake zaune a nan.

Genesis 38:24

Menene Yahuda ya na so ya sani a lokacin da ya ji cewa Tama ta na da ciki?

Yahuda ya so ya ƙona ta domin ta yi ciki a karuwanci.

Menene Tama ta yi a lokacin da aka kawo wurin Yahuda?

Ta faɗa cewa ta yi ciki da mutum mai wannan zoben tambarin da ɗamarar da sandar da take da su.

Yay ne Yahuda ya amsa a lokacin da ya gan zoben tambarin da ɗamarar da sandar dinsa?

Yahuda ya gane Tama ta fi shi adalci, tunda bai ba da ita a matsayin mata ga Shela, ɗansa ba.

Genesis 38:27

'Yaya nawa ne Tama ta haifa?

Tama ta haifa tagwaye.

Menene matan unguwar zomar suka yi a lokacin da ɗaya daga cikin tagwayen ya fitar da hannunsa waje?

A lokacin da ɗaya daga cikin tagwayen ya fitar da hannunsa waje, matan nguwar zomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura masa a hannu ta kuma ce, "Wannan ne ya fãra fitowa."

Genesis 38:29

Menene sunayen 'yan'uwa biyu da Tama ta haifa?

Sunayen 'ya'ya biyu da Tama ta haifa su ne Ferez da Zerah.