Genesis 27

Genesis 27:1

Sa'adda Ishaku yayi girma, menene bai iya yi kuma ba?

Sa'adda Ishaku yayi girma, bai iya gani ba.

Genesis 27:3

Menene Ishaku ya ce ma Isuwa yayi, kuma don menene?

Ishaku ya ce ma Isuwa ya je farauta ya kuma yi masa irin abincin da yake so domin ya iya ci ya kuma albarkace shi.

Genesis 27:8

Menene shirin Rebeka domin tanada wa Ishaku abinci, kuma don menene?

Rebeka ta faɗa wa Yakubu cewa ya je ya sami awaki guda biyu kuma zata yi abincin da Ishaku na so sosa, domin Yakubu ya iya kai wa Ishaku ya kuma ƙarbi albarkan.

Genesis 27:11

Game da menene Yakubu ya damu da kawo abincin wa Ishaku?

Yakubu ya damu cewa Isuwa mutum mai gargasa ne kuma shi sulɓi ne. Kuma Ishaku zai taɓa shi, zai kuma gane cewa Yakubu mayaudari ne ya kuma la'anta shi.

Genesis 27:15

Yaya ne Rebeka ta warware damuwar Isuwa mai gargasa da Yakubu sulɓin mutum?

Rebeka ta sa ma Yakubu tufafin Isuwa ta kuma sa mashi fatar 'yan awaki a hannunsa da kuma tattausan sashen wuyansa.

Genesis 27:20

Sa'adda Ishaku ya tambaya, yaya ne Yakubu ya ce ya samo dabban da sauri?

Yakubu ya faɗa cewa, Yahweh Allansa ya kawo masa.

Genesis 27:22

Domin bai tabbatar ba, yaya ne Ishaku yayi kokarin sanin wanda ke bashi abinci?

Ishaku ya taɓa Yakubu a kai sai ya ji gashin akuyan.

Genesis 27:24

Menene Yakubu ya faɗa a lokacin da Ishaku ya ce, "Kai ne ɗana Isuwa kuwa?"

Yakubu ya ce, "Ni ne."

Genesis 27:26

Menene ya tabbatar wa Ishaku cewa mutumin da ke kawo abincin Isuwa ne?

Sa'adda Yakubu ya matso kusa ya sumbace shi ya sunsuni ƙamshin suturar Isuwa.

Genesis 27:29

Wanene Ishaku ya ce zai rusuna wa Yakubu?

Ishaku ya ce al'ummai zasu rusuna masa kuma 'ya'yan mahaifiyar shi maza zasusu rusuna masa.

Genesis 27:30

Menene Isuwa yayi bayan Yakubu ya bar wurin Ishaku?

Isuwa ya shigo daga wurin farauta, ya shirya abinci mai daɗi ya kawo wa Ishaku.

Genesis 27:34

Menene Ishaku ya faɗa a lokacin da Isuwa ya roƙa albarkansa?

Ishaku ya ce Yakubu ya zo cikin yaudara ya karɓe albarkar Isuwa.

Genesis 27:36

A wane hanyoyi biyu ne Isuwa ya ce Yakubu ya cuce shi?

Isuwa ya faɗa cewa Yakubu ya cuce daga matsayinsa na ɗan fãri, da kuma albarkansa.

Genesis 27:39

Menene "Albarka" da Ishaku ya ba wa Isuwa?

Ishaku ya faɗa cewa Isuwa zai zauna da nisa daga wadatar duniya, zai bautawa ɗan'uwansa, amma zai tayar ya kawar da karkiyarsa daga wuyan Yakubu.

Genesis 27:41

Menene Isuwa ya shirya yi bayan mutuwar Ishaku?

Isuwa ya shirya ƙashe Yakubu bayan mutuwar Ishaku.

Genesis 27:43

Menene Rebeka ta yi bayan jin shirin Isuwa?

Rebeka ta aika Yakubu wurin Laban ɗan'uwanta a Haran.