Genesis 8

Genesis 8:1

Ya ya ne Allah ya sa ruwan ya sauka?

Allah ya sa iska ta hura a, maɓuɓɓugai na ƙarƙas da sakatun sama aka rufe su sai ruwan ta daina.

Genesis 8:4

Ina ne jirgin ya zo ya shaƙatawa a ƙasan?

Jirgin ya zo ya shaƙatawa a a kan duwatsun Ararat.

Genesis 8:8

Menene ya faru a farkon da Nuhu ya aiki kurciya daga jirgin?

A farko, kurciyan bata sami wurin hutawa ba, sai ta dawo wurin Nuhu a jirgin.

Genesis 8:10

Menene ya faru na biyu da Nuhu ya aiki kurciya daga jirgin?

Na biyu, kurciya ta dawo wurinsa da ganyen zaitun.

Menene ya na uku a farkon da Nuhu ya aiki kurciya daga jirgin?

A na uku, kurciyan bata sake dawo wurin Nuhu ba

Genesis 8:13

Menene Nuhu ya gani a lokacin da ya buɗe rufin jirgin sai ya daba waje?

Nuhu ya gan cewa ƙasa ta bushe.

Genesis 8:15

Menene Allah ke son dukka halitta a cikin jirgin su je su yi sa'adda sun bar jirgin?

Allah ya so dukka hallitta su hayayyafa, su kuma ruɓanɓanya a cikin duniya.

Genesis 8:20

Menene Nuhu yayi a lokacin da ya bar jirgin?

Nuhu ya gina bagadi ga Yahweh sai ya miƙa hadaya akan bagadin.

Wane alkawari biyu ne Allah ya yi wa ɗan mutum a wannan lokacin?

Allah yayi alkawari cewa ba zai sake la'anta ƙasa ba, kuma ba zai ƙara hallakar da duk masu rai ba.

Menene Allah ya ce tunanin mutum yake tun daga yarintaka?

Allah ya ce tunanin mutum tun daga yarintaka mugunta ne.