Genesis 7

Genesis 7:1

Wane irin dabbobi bakwai ne mata da maza za su shiga jirgin?

Dabbobi bakwai na maza da mata na kowane iri masu tsarki da kuma tsuntsaye zasu tafi a cikin jirgin.

Genesis 7:4

Menene tsawon lokacin da Allah ya ce ruwan saman zai cigaba a duniya?

Allah ya faɗa cewa ruwan sama zai cigaba kwana arba'in dare da rana.

Genesis 7:6

Shekarun Nuhu nawa ne a lokacin da ruwan tsufana ya zo duniya?

Nuhu ya na da shekaru ɗari shidda a lokacin da aka yi ruwan tsufana a duniya.

Genesis 7:8

Yaya ne Nuhu ya kawo dabbobin cikin jirgin?

Dabbobin sun zo wurin Nuhu sai suka shiga cikin jirgin.

Genesis 7:11

Daga wurare nawa ne ruwan tsufanan suka fito?

Ruwan sun zo daga taskoki na zurfafa da kuma daga sarari.

Genesis 7:15

Sa'adda dukka mutane da dabbobi suna cikin jirgin, wanene ya kulle ƙofan?

Yahweh ya kulle ƙofar.

Genesis 7:19

Yaya ne tudun ruwan a kai a duniya?

Ruwan ya kai har taki shidda a bisa duwatsu.

Genesis 7:21

Domin tsufanan, menene ya mutu akan duniyan?

Dukkan halittu da ke motsi bisa duniya da dukka mutane suka mutu.

Genesis 7:23

Su wanene mutane da suka rayu a duniyan?

Nuhu ne kadai da waɗanda suke tare da shi a cikin jirgin suka rayu.