Genesis 13

Genesis 13:1

Zuwa ina ne Abram yayi tafiya bayan barin Masar?

Abram ya yi tafiya zuwa Negeb.

Menene Abram ya ɗauki da shi?

Abram ya ɗauka da shi dabbobi dayawa da kuma zinariya da azurfa da yawa.

Genesis 13:5

Don menene akwai rashin jituwa tsakanin makiyayan dabbobin Ibram da kuma makiyayan dabbobin Lot?

Akwai rashin jituwa domin ƙasar ba ta iya ɗaukar Abram da Lota tare da dukka mallakarsu ba.

Genesis 13:8

Wane tayi ne Abram yayi wa Lot?

Abram yayi wa Lot tayi cewa ya zaɓa inda zai zauna, sai ya nemi wurin zamansa dabam da Lot.

Genesis 13:10

Ina ne Lota ya zaɓa ya zauna kuma don menene?

Lot ya zaɓi ya tafi gabas ya zauna a filin na Urdun domin an shayar da shi.

Genesis 13:12

Ina ne Abram ya zauna?

Abram ya zauna a ƙasar kanaan.

Wane irin mutanen ke zama a Saduma?

Mutanen Saduma miyagu ne masu yi wa Yahweh zunubi.

Genesis 13:14

A wannan lokacin, Menene Yahweh ya de zai ba wa Abram?

Yahweh ya yi alkawari cewa zai ba wa Abram dukka ƙasar da yake gani daga inda yake tsaye.

Genesis 13:16

Zuriya nawa ne Yahweh ya ce Abram zai samu?

Yahweh ya ce Abram zai sami zuriya fiye da yadda zai iya ƙirga " haɓaka kamar turɓayar ƙasa."

Kusa da wane ƙasa ne Abram ya je?

Abram ya je kusa da birnin Hebiron.