Genesis 12

Genesis 12:1

Sa'adda Abram na zama a Haran, menene Yahweh ya ce masa ya yi?

Yahweh ya faɗa wa Abram ya bar gidan mahaifinsa ya kuma tafi zuwa ƙasar da zai nuna masa.

Wane alkawari ne Yahweh ya yi wa Abram?

Yahweh yayi alkawari cewa zai albarkaci Abram, zai maishe shi babbar al'umma, ya kuma albarkaci dukka iyalin duniya ta wurinsa.

Genesis 12:4

Wanene yayi tafiya da Abram?

Abram yayi tafi da Sarai matarsa, da kuma Lota, ɗan ɗan'uwansa.

Zuwa wane ƙasa ne Abram yayi tafiya?

Abram yayi tafiya zuwa ƙasar Kanaan.

Genesis 12:6

A lokacin da Yahweh ya bayyana wa Abram, wane alkawari ne ya yi wa Abram?

Yahweh ya yi alkawari cewa zuriyar Abram zasu zauna a Kanaan.

Genesis 12:8

Ya ya ne Abram ya bauta wa Yahweh?

Abram ya gina bagadi wa Yahweh ya kuma kira ga sunar Yahweh.

Genesis 12:10

Barin Kanaan, zuwa ina ne Abram ya yi tafiya?

Barin Kanaan, Ibrahim yayi tafiya zuwa Masar.

Game da menene Abrahim ya damu sa'adda ya shiga Masar?

Abram ya damu cewa Masarawa zasu kashe shi su kuma ɗauki matarsa Sarai domin kyaukyauwa ce.

Menene Abram ya ce wa Sarai ta faɗa wa Masarawa game da kanta?

Abram ya ce wa Sarai ta faɗa wa Masarawa cewa ita 'yar'uwarsa ce.

Genesis 12:14

Menene ya faru da Sarai sa'adda suka shiga cikin Masar?

Fir'auna ya ɗauke Sarai zuwa cikin gidansa.

Genesis 12:17

Menene ya faru da Fir'auna a wannan lokacin?

Yahweh ya bugi Fir'auna da gidansa da annoba mai zafi.

Wane tambaya ne Fir'auna ya yi wa Abram?

Fir'auna ya tambaye Abram dalilin da ya sa ya ce Sarai 'yar'uwarsa ce a maimakon matarsa.

Menene Fir'auna yayi da Abram da Sarai?

Fir'auna ya sallame Abram da Sarai.