Genesis 9

Genesis 9:1

Menene Allah yace wa Nuhu da 'ya'yansa su yi bayan sun bar jirgin?

Allah yace wa Nuhu da 'ya'yansa su ruɓanɓanya ku hayayyafa su kuma ciki duniya.

Genesis 9:3

Menene Allah ya ba wa Nuhu da 'ya'yansa a matsayin abinci?

Allah ya ba wa Nuhu da 'ya'yansa koren ganyaye da dukkan wani abi mai motsi dake rayuwa a matsayin abinci.

Yaya ne Allah ya umarce naman da ba za a ci ba?

Allah ya umarci cewa kada a ci nama da jini a cikinsa.

Menene Allah ya ce ke cikin jinin?

Allah ya faɗa cewa akwai rai a cikin jinin.

Genesis 9:5

Menene Allah ya ayana cewa shine hukuncin zub da jinin mutum?

Allah ya ayana cdewa wanda ya zubar da jinin mutum ta wurin mutum za a zubar da jininsa.

A cikin kamannin wanene Allah ya yi mutum?

Allah ya yi mutum a cikin kamanninsa.

Genesis 9:11

Wane alama ne Allah ya bayar don alkawarin da ya yi da duniya?

Allah ya sa bakangizona a cikin girgije, zai zama alamar alkawarinsa da yayi da duniya.

Genesis 9:14

Wane alkawari ne Allah ya yi da dukka abin da ke zama a duniya?

Allah yayi alkawari cewa ba za a sake hallaka dukka mai rai ba.

Genesis 9:18

Menene sunayen 'ya'yan Nuhu?

Sunayen 'ya'ya uku na Nuhu sune Shem, Ham, da kuma Yafet.

Genesis 9:20

Menene ya faru da Nuhu bayan ya shuka garkar inabi?

Bayan ya shuka garkar inabi, Nuhu ya sha waɗansu 'ya'yan inabin ya kuma bugu.

Genesis 9:22

Ya ya ne Shem da Yafet suka rufe tsiraicin mahaifinsu?

Shem da Yafet sun yi tafiya da baya da mayafi, sa'adda suke juya wani gefen domin su rufe tsiraicin mahaifinsu.

Genesis 9:24

Menene la'ana da Nuhu ya sa wa Ham?

Nuhu ya la'anta Ham ya kuma ce, "Kan'ana ta zama la'annanne.Bari ya zama baran barorin 'yan'uwansa.''

Genesis 9:26

Wanene Nuhu ya albarkace?

Nuhu ya albarki Shem da kuma Yafet.