Genesis 6

Genesis 6:1

Sa'adda ɗan mutum suka ruɓamɓanya a duniya, menene 'ya'yan Allah suka yi?

'Ya'yan Allah suka auri mata daga 'ya'ya mata na ɗan mutum.

Menene yanzu Allah ya faɗa game da tsawon ran ɗan mutum?

Allah ya faɗa cewa ɗan mutum zai rayu shekaru 120 ne.

Genesis 6:4

Su wanene manyan mutanen dă, ƙarfafan mutane?

Manyan mutanen dă, su ne ƙarfafan da aka haife su daga 'ya'yan Allah da sun auri 'ya'ya mata na mutane.

Genesis 6:5

Menene Yahweh ya gani daga zuciyar ɗan mutum a waɗannan lokacin?

Yahweh ya ga cewa muguntar mutum ta haɓaka, kuma dukkan tunane tunanensa zukatansu mugunta ce.

Genesis 6:7

Menene Yahweh ya shirya zai yi wa ɗan mutum?

Yahweh ya shirya zai shafe mutum daga fuskar duniya.

Amma wanene ya sami tagomashi daga Yahweh?

Nuhu ya sami tagomashi da Yahweh.

Genesis 6:9

Wane irin mutum ne Nuhu?

Nuhu adalin mutum ne, mara abin zargi kuma yayi tafiya tare da Allah.

Genesis 6:13

Menene Allah ya ce wa Nuhu yayi kafin Allah ya hallaka ɗan mutum?

Allah ya ce wa Nuhu ya gina jirgi.

Genesis 6:16

Ya ya ne Allah ya ce zai hallaka dukka masu rai dake da numfashi?

Allah ya faɗa cewa zai kawo tumbatsar ruwa a duniya.

Genesis 6:18

Amma da wanene Allah ya kafa alkawarinsa?

Allah ya kafa alkawarinsa da Nuhu.

Wanene Allah ya ce wa Nuhu ya kawo cikin jirgin?

Allah ya faɗa wa Nuhu cewa ya kawo matarsa, 'ya'yansa uku, da kuma matan 'ya'yansa.

Wane dabbobi ne za a kawo cikin jirgin don su rayu?

Kowanne iri biyu na hallitu, namiji da mace, aka kawo cikin jirgin.

Genesis 6:20

Ya ya ne Nuhu ya amsa umarnin Allah?

Nuhu yayi dukka abinda Allah ya umarce shi.