Genesis 4

Genesis 4:1

Wane aiki ne Kayinu da Habila suke yi?

Habila makiyayi ne, kuma Kayinu manomi ne.

Genesis 4:3

Wane hadaya ne Kayinu ya kawo wa Yahweh?

Kayinu ya kawo amfanin gonar daga ƙasa.

Wane hadaya ne Kayinu ya kawo wa Yahweh?

Habila ya kawo waɗansu 'ya'yan fari daga cikin garkensa da kuma sashe na kitse.

Ya ya ne Yahweh ya amsa wa hadayun Kayinu da Habila?

Yahweh ya karɓi hadayan Habila, amma bai karɓa hadayan Kayinu ba.

Ya ya ne Kayinu yayi?

Kayinu ya fusata sosai, ya kuma ɓata fuska.

Genesis 4:6

Menene Yahweh ya ce wa Kayinu ya kamata ya yi domin ya sami ƙarbuwa?

Yahweh ya ce wa Kayinu yayi abin nagari sai a ƙarbe shi.

Genesis 4:8

Bayan haka, menene ya faru da Kayinu da Habila a gonar?

Kayinu ya tashi ya kashe Habila.

Sa'adda Yahweh ya tambayi Kayinu inda ɗan'uwansa yake, menene Kayinu ya ce?

Kayinu ya ce, "Ban sani ba. ni makiyayin ɗan'uwana ne?"

Genesis 4:10

Menene la'anar Allah akan Kayinu?

La'anar Kayinu shine ƙasar baza ta ba ka issashen amfaninta ba, kuma zai zama mai yawo barkatai.

Genesis 4:13

Menene Yahweh ya yi domin ya tabatar cewa wani bai kashe Kayinu ba?

Yahweh ya sa alama akan Kayinu.

Genesis 4:16

Ina ne Kayinu ya je zama?

Kayinu ya zauna a ƙasar Nod, a gabashin Adinin.

Genesis 4:18

Zuriyar Kayinu, Lamek na da mata nawa?

Lamek na da mata biyu.

Genesis 4:23

Menene Lamek ya faɗa wa matansa cewa yayi?

Lamek ya faɗa wa matansa cewa ya kashe mutum.

Genesis 4:25

Menene wani sunar ɗan da aka sake haifa wa Adamu da Hawa?

Wani sunar ɗan Adamu da Hawa shine Set.

Menene mutane suka fara yi a lokacin ɗan Set, Enosh?

Mutane suka fara kira ga sunar Yahweh.