Genesis 2

Genesis 2:1

Menene Allah yayi a rana ta bakwai?

Ya huta daga dukkan aikinsa, sai ya albarkaci rana ta bakwai ya kuma tsarkaketa.

Genesis 2:4

Kafin Yahweh ya sa a yi ruwan sama, ya ya ne ake jiƙa ƙasa?

Raɓa na sauka daga ƙasa.

Genesis 2:7

Ta ya ya ne Yahweh ya hallici mutum?

Yahweh Allah ya halitta mutum daga cikin ƙasa, ya kuma hura masa numfashin rai.

Ina ne Yahweh ya fara sa mutumin a farko?

A cikin lambun Adinin.

Genesis 2:9

Wane itatuwa uku ne suke tsakanin lambun?

Itacen rai da itacen sanin mugunta da nagarta.

Genesis 2:15

Menene mutumin zai yi a lambun?

Zai nome ya kuma kula da lambun.

Wane umarni ne Yahweh ya ba wa mutumin game da abin da zai ci?

Kana da 'yancin cin kowanne irin 'ya'yan itace na cikin lambun amma ban da itace na sanin nagarta da mugunta ba.

Menene Yahweh ya ce zai faru idan mutum ya ƙeta umarnin?

A ranar da mutumin ya ƙeta umarnin, zai mutu.

Genesis 2:18

Menene Yahweh ya ce ba shi da kyau?

Yace ba shi da kyau mutum ya zauna shi kaɗai.

Menene Yahweh ya sa mutumin yi da kowanne hallita?

Mutumin ya ba kowacce halitta suna.

Menene ba a samu a cikin dukka hallita?

Mataimakiya mai dacewa da shi.

Genesis 2:21

Yaya ne Yahweh yayi macen?

Yahweh ya sa mutumin barci sai ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa sai ya yi mace daga haƙarƙarin.

Don menene mutumin ya kira ta "mace"?

Saboda daga jikin mutumin aka ciro ta.

Genesis 2:24

Yaya ne miji da mace ke zama jiki ɗaya?

Mutumin na saduwa da macen a matsayin matsarsa.

Mutumin da matarsa sun ji kunyar tsiraicinsu?

A'a.