Genesis 22

Genesis 22:1

Sai ya zamana

Ana amfani da wannan a sa alama a farkon sashin labarin ne. Idan harshen ku na yadda ake faɗin wannan, yana iya yiwuwa a yi amfani da shi a nan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-newevent)

bayan waɗannan abubuwa

Wannan kalmar na nufin abin da ya faru a Farawa Sura 21 ne.

Allah ya gwada Ibrahim

An nuna cewa Allah yana gwada Ibrahim don ya sani ko Ibrahim zai kasance da aminci a gare shi. Cikakkiyar ma'anar wannan bayanin za a iya bayyana a sarari. AT: "Allah ya gwada amincin Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Gani nan

"Na'am, ina saurara"

tilon ɗanka

Wannan na nuna cewa Allah ya san wai Ibrahim na da wani yaro, Isma'ila. Wannan na jadada cewa Ishaku ne ɗan alkawarin da Allah ya ba wa Ibrahim. Cikakkiyar ma'anar wannan bayanin za a iya bayyana a sarari. AT: "tilon ɗanka da na alkawatar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

wanda ka ke ƙauna

Wannan na jadada ƙaunar da Ibrahim ya ke da shi ga ɗansa Ishaku.

ƙasar Moriya

"ƙasar da ake kira Moriya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ɗaura wa jakinsa sirdi

"ɗaura wa jaki kaya" ko "sa kayan da ya ke bukata domin tafiyar a kan jaki"

matasa biyu

"bayi" (UDB)

ya kama hanyarsa

"fara tafiyar sa" (UDB)

Genesis 22:4

A rana ta uku

AT: "bayan tafiya na tsawon kwanaki uku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

hangi wurin daga nesa

"ya hangi daga nesa inda Allah ya faɗa"

Zamu yi sujada

Kalmar "mu" na nufi Ibrahim da Ishaku kawai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)

dawo wurinku

"komo gare ku"

ɗora wa Ishaku ɗansa

"ya sa Ishaku, ɗansa ya ɗauka"

ya ɗauki a hannunsa

"A hannunsa" na jadada cewa Ibrahim ya ɗauka waɗannan abubuwan da kansa. AT: "Ibrahim da kansa ya ɗauki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

wutan

Anan "wuta" na nufin kwano da garwashin wuta a ciki ko fitila. AT: "wani abu da ake wura wuta" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sai kuma su ka tafi tare

"suka tafi tare" ko "suka tafi tare su biyu"

Genesis 22:7

Babana

Wannan hanya ce da ɗa ke maganar da mahaifinsa cikin ƙauna.

Gani nan

"Na'am, ina saurara" ko "Na'am, me ya faru?"

ɗana

Wannan hanya ce da mahaifi ke magana da ɗansa cikin ƙauna.

ragon baikon ƙonawa

"ragon da za ka mika baikon ƙonawar?"

Allah da kansa

"Kansa" a nan na jadada cewa Allah ne zai tanada ragon. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rpronouns)

zai tanada

"zai ba mu"

Genesis 22:9

Sa'ad da su ka zo wurin

"Sa'ad da Ibrahim da Ishaku su ka iso wurin"

akan bagadin bisa itacen

"a bisa itacen da ke kan bagadi"

ya miƙa hannunsa ya ɗauko wuƙa

"ɗauki wuƙa"

Genesis 22:11

Sai mala'ikan Yahweh

Ma'ana mai yiwuwa 1) Yahweh ya mayar da kansa a kamanin mala'ika, ko 2) wannan ɗaya ne daga cikin mala'ikun Yahweh, ko 3) wannan da aika ne daga Allah na musamman (Wasu masu karatu na tunani Yesu ne). Tunda shike maganar ba fili ta ke, zai fi kyau a juya yadda ya ke "mala'ikan Yahweh" kamar yadda aka saba amfani da kalmar "mala'ika." Duba Farawa 16:7.

Kada ka ɗora hannunka a kan yaron, kar ka yi duk wani abu da zai cutar da shi

Kalmar "kada ka ɗore hannunka a kan" wata hanyar cewa "kada ka cutar." Allah na maimata abu ɗaya sau biyu domin ya jadada cewa kada Ibrahim ya yi wa Ishaku illa. AT: "kada ka cutar da yaron ta kowani hanya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)

yanzu na sani ... daga gare ni

Kalmomi "Na" da "Ni" na nufin Yahweh ne. A sa'ad da ana fassara wannan, sai a yi shi kamar yadda mala'ikan Yahweh ya yi amfani da kalmomin "Na' da "Ni" wajen nufin Yahweh.

kana tsoron Allah

Wannan na nufin ba da girma ga Allah da kuma nuna wannan girmar wajen yin biyyaya a gare shi.

ganin cewa

"domin na ga cewa"

ba ka hana mini ɗanka ba

"ba ka hana ɗanka ba ... daga gare ni." AT: "kana shirye ka miƙa ɗanka ... a gare ni" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublenegatives)

Genesis 22:13

duba

Kalmar "duba" na jawo hankalin mu ne ga bayani da ke zuwa.

ɗan rago a sarƙafe da ƙahonsa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "ɗan rago da ƙahonsa ya makale a daji" ko "ragon da ya makale da daji" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ya ɗauki ɗan ragon

"Ibrahim ya je ya ɗauki ragon"

zai tanada ... za a tanada

A amfani da kalma ɗaya da aka yi amfani da shi a Farawa 22:7.

har a yau

"har yanzu." Ma'anar wannan shine har zuwa lokacin da marubucin ke rubuta wannan littafin.

za a tanada

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "zai tanada" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 22:15

na biyu

Kalmar "na biyu" ita ce ƙa'ida ta biyu. AT: "sake" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-ordinal)

kuma yace - wannan shi ne furcin Yahweh

"faɗa saƙon nan daga Yahweh" ko "furta waɗannan kalmomin daga Yahweh." Wannan na nufin cewa maganar ta zo daga Yahweh ne kai tsaye.

na yi rantsuwa da kaina

"Na yi alkawari kuma ni ne shaida." Kalmar "rantsuwa da" na da ma'anar wani abu ko wani mutum da shine tushi ko na da iko bisa alkawarin da aka yi. Ba wani abu da ke da iko fiye da Yahweh da zai yi rantsuwa da shi.

ka yi wannan abu

"ka yi mini biyyaya"

zan kuma ruɓanɓanya zuriyarka

"Zan sa zuriyarka su yi ta karuwa" ko "Zan sa zuriyar ka su yi yawa"

kamar taurarin sammai, kamar kuma yashin da ke gaɓar teku

Allah na kamanta yawan zuriyar Ibrahim da taurari da yashi. Kamar yadda mutane ba za su iya kirga taurari ko yashi ba, haka zuriryar Ibrahim za su yawa da mutane ba za su iya kirga wa ba. AT: "fiye da abun da za ka iya kirgawa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)

kamar taurarin sammai

"sammai" a nan na nufin dukka abun da ke sama da duniya, da rana, wata, da kuma taurari.

za su mallaki ƙofar maƙiyansu

Anan "ƙofar" na wakiltar birnin gaba ɗaya. "mallaki ƙofar maƙiyansu" na ma'anar hallakar da aƙiyansu. AT: "samu cikaken nasara bisa maƙiyansu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 22:18

Muhimmin Bayani:

Mala'ikan Yahweh ya ci gaba da magana da Ibrahim.

za a albarkaci dukkan al'ummar duniya

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Ni, Ubangiji, zan albarkaci duk mutanen da ke zaune a ko'ina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ka yi biyayya da muryata.

Anan "murya" na nufin abun da Allah ya faɗa. AT: "ka yi biyyaya da abun da na faɗa" ko "ka yi mini biyyaya" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Ibrahim ya koma

An ambata sunan Ibrahim ne kadai domin shine uban, amma a nufin cewa ɗansa ya koma tare da shi. Ana iya ba da cikakiyar ma'anar wannan maganar a fili. AT: "Ibrahim da ɗansa suka koma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

suka tafi

"suka bar wacan wurin"

ya zauna a Biyasheba

An ambaci Ibrahim shi kadai domin shine shugaban iyalinsa da barorinsa, amma a nufin cewa suna tare da shi ne. Cikakiyar ma'anar wannan magana na a fili haka. AT: "Ibrahim da mutanen sa suka zauna a Biyasheba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 22:20

Sai ya zamana bayan waɗannan abubuwa

"Bayan waɗannan abubuwan." Maganar "waɗannan abubuwa" na nufin aukuwar Farawa 22:1-19. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-newevent)

aka ce da Ibrahim

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Wani ya ce da Ibrahim" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

haka kuma Milka ta haifi 'ya'ya,

"Milka ma ta haifi 'ya'ya"

Su ne Uz ɗansa na fari, Buz shi ne ɗan'uwansa

"Sunan ɗansa na fara shi ne Uz, sunan sauran 'ya'yansa kuma Buz ne ɗan'uwansa"

Uz ... Buz ... Kemuwal ... Aram ... Kesed, Hazo, Fildash, Jidlaf da Betuwel

Waɗannan sunayen maza ne. Juya waɗannan yadda za a gane a fili cewa dukka waɗannan 'ya'yan Nahor ne da Milka, banda Aram. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Genesis 22:23

Betuwel ya haifi Rebeka

"Daga baya Betuwel ya zama mahaifin Rebeka"

Waɗannan su ne 'ya'ya takwas da Milka ta haifa wa Nahor, ɗan'uwan Ibrahim

"Waɗannan takwas sune 'ya'yan Milka da Nahor ɗan'uwan Ibrahim."

Ƙwarƙwararsa

"Ƙwarƙwarar Nahor"

Reuma

Wannan sunan mace ce. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Tebah, Gaham, Tahash da Ma'aka

Waɗannan sunayen mazaje ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)