Genesis 21

Genesis 21:1

Yahweh ya saurari Sarai

Kalmar "saurari" a nan na nufin cewa Yahweh ya taimakawa Sarai wajen samun ɗa. AT: "Yahweh ya taimakawa Sarai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ta haifa wa Ibrahim ɗa

"ta haifa ɗa wa Ibrahim"

a cikin kwanakin tsufansa

"sa'ad da Ibrahim ya tsufa kwarai"

a dai-dai lokacin da Yahweh ya yi masa magana

"a dai-dai lokacin da Allah yace da shi zai faru"

Ibrahim kuma ya raɗa wa ɗansa suna, wato wannan ɗa da aka haifa masa, wannan da Sarai ta haifa masa wato Ishaku

"Ibrahim ya sa wa ɗan jariri da aka haifa masa, wanda Sarai ta haifa, Ishaku" ko "Ibrahim ya ba sunan ɗan su Ishaku"

da ya yi kwana takwas, Ibrahim ya yi wa ɗansa Ishaku kaciya

"Sa'ad da Ishaku ɗansa na kwana ta takwas, Ibrahim ya yi masa kaciya"

ya umarce shi

"ya umarce Ibrahim ya yi"

Genesis 21:5

shekaru ɗari

"100" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

Allah ya sa ni dariya

Sarai na dariya domin tana murna da kuma mamaki. Ana iya bayana wannan haka. AT: "Allah ya sa ni farin ciki" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

duk wanda ya ji

Ana iya ba da gamsashen bayani game da abin da mutane za su ji. AT: "duk wanda ya ji abin da Allah ya yi mini" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Wane ne zai ce da Ibrahim cewa Sarai za ta yi masa renon 'ya'ya

Ana iya fassara wannan tambayar a matsayin sanarwa. AT: "Ba wanda zai ce da Ibrahim, Sarai za ta reno 'ya'ya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

renon 'ya'ya

Wannan wata hanya ne cikin da'a da ake nufi da shayas da 'ya'ya. AT: "shayas da jariri da nono ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Genesis 21:8

Yaron ya yi girma ... aka yaye Ishaku

"yaye" a nan hanya ce mai ladabi na cewa yaron ya gama da nono. AT: "Ishakuya girma kuma baya bukatar shan nono mahaifiyarsa. Ibrahim ya yi babbar liyafa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

ɗan Hajara mutumiyar Masar da ta haifa wa Ibrahim

Ana iya ambaci sunan ɗan Hajara. AT: "Isma'ila ɗan Hajara na Masar da Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

ba'a

Ana iya bayana cewa ya na yi wa Ishaku ba'a. AT: "yi wa Ishaku dariya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 21:10

ta ce da Ibrahim

"Sarai ta cewa Ibrahim

Ka kori

"salleme" ko "cire" (UDB)

baiwar matar da ɗanta

Wannan na nufin Hajara ne da Isma'ila. Mai yiwuwa Sarai ba ta ambaci su da sunayen su domin tana fushi da su.

tare da ɗa na Ishaku

"tare da ɗa na Ishaku"

Wannan abin ya yi wa Ibrahim zafi

"Ibrahim bai ji dadin abin da Sarai ta faɗa ba"

saboda ɗansa

"domin ta magana game da ɗan sa." Ana nufin da ɗan sa, Isma'ila. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Genesis 21:12

Kada ka damu saboda yaron, da kuma saboda wannan matar baiwarka

"Kada ka yi fushi game da yaron da baiwarka"

Ka saurari kalmominta kan duk abin da ta faɗa maka kan wannan al'amari

AT: "Ka yi duk abin da Sarai ta ce da kai game da su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ta wurin Ishaku ne za a kira zuriyarka

Kalmar "za a kira" na nufin cewa waɗanda aka haifa ta wurin Ishaku ne Allah zai yi amfani da su a matsayin zuriyar alkawari da Ibrahim. AT: "Ishaku ne zai kasance kakan zuriyar da na alkawatar ma ka" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Hakanan zan sa ɗan baiwar matar ya zama al'umma

Kalmar "al'umma" a nufin cewa Allah zai ba shi zuriya mai girma da za su zama babban jama'a. AT: "Zan sa ɗan baiwar ma ya zama uban babban al'umma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 21:14

ya ɗauki gurasa

Ma'ana mai yiwuwa 1) wannan na nufi kowani irin abinci, ko 2) gurasa ne musamman. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

goran ruwa

"jakar ruwa." Ana yin gorar ruwa da fatar dabba.

Da ruwan da ke cikn goran ruwan ya ƙare

"da ruwan gorar ya ƙare" or "da su ka sha ruwar dukka"

nesa dai-dai harbin kibiya

Ma'anar wannan shine, nesa kamar harbin kibiya. Wannan na kamar mita 100.

Kada in ga mutuwar ɗa na

AT: "Ba na so in ga yadda yaron zai mutu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

sai ta ta da murya ta yi kuka

Anan "murya" tana tsaye don sautin kukanta. AT: ta ta da babban murya ta yi kuka" ko "ta yi kuka da karfi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Genesis 21:17

muryar yaron

"muryar yaron." Anan "murya" na nufin karar kuka or maganar yaron. AT: "muryar Isma'ila" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

daga can sama

"sama" a nan na nufin inda Allah ya kasance.

Me ke damun ki

"Don me ki na kuka"

muryar ɗan a inda ya ke

Anan "murya" tana tsaye don sautin yaron yana kuka ko magana. AT: "muryar yaron a kwance a wurin"' (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

tashi ki ɗauki yaron

"taimake yaron ya tashi tsaye"

Zan maishe shi babbar al'umma

Ma'anar maishe Isma'ila babbar al'umma shine zuriyarsa za su zama babbar al'umma. AT: "Zan mai da zuriyarsa babban al'umma" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 21:19

Allah ya buɗe idanunta, sai ta ga

An yi maganar yadda Allah ya sa Hajara ta ga rijiyar kamar ya ɗau hannunsa ne ya buɗe idanunta. AT: " Allah ya sa Hajara ta ga" ko "Allah ya nuna mata" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

fatan

"gorar fata" ko "jaka"

ɗan

"yaron" ko "Isma'ila"

Allah na tare da ɗan

Ma'anar wannan maganar "tare da" shi ne Allah ya taimakawa ko ya sa wa ɗan albarka. AT: "Allah ya kulla da yaron" ko "Allah ya sa wa yaron albarka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

zama mafarauci

"gwanancewa a amfani da baka da kibiya"

aura masa mata

"samo masa mata"

Genesis 21:22

Sai ya zamana a lokacin

Wannan maganar na nuna farkon wani sabon sashin labarin ne. Idan harshenku na da yadda kuke faɗin wannan, ana iya amfani da shi a nan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-newevent)

Fikol

Wannan sunan namiji ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

Allah na tare da kai a cikin dukkan al'amuranka

Wannan maganar "tare da kai" na ma'anar cewa Allah ya taimake ko albarkaci Ibrahim. AT: "Allah ya albarkaci ayyukan ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Yanzu fa

Wannan kalmar "yanzu" baya ni "a dai-dai wannan lokacin", amma an yi amfani da shi ne wajen jawo hankali ga maganar da ke zuwa. AT: "Saboda haka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

rantse mini da Allah

Ma'anar wannan shi ne rantsuwa da babban iko, a wannan wurin kuma, Allah ne. AT: "yi mini alkawari a gaban Allah" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

cewa ba za ka yi mini ƙarya ba

"cewa ba za kayi mun karya ba"

Ka nuna mini ... alƙawari mai aminci da na nuna gare ka

Mutane biyun suna da alkawari a tsakanin su. AT: "kasance da aminci a gare ni da kuma kasar, kamar yadda na yi a gare ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

ƙasar

Anan "ƙasar" na wakiltar mutane. AT: "ga mutanen ƙasar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Na ranste

Ana iya bayyana wannan tare da bayanan da aka fahimta. AT: "Na rantse zan yi maka aminci da mutanenka kamar ya ka ke mini" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

Genesis 21:25

Ibrahim kuma ya miƙa kukansa ga Abimelek

Ma'ana mai yiwuwa 1) Ibrahim na kokawa game da abin da ya faru, ko 2) "Ibrahim kuma ya tsawata wa Abimelek"

game da rijiyar ruwa da bayin Abimelek su ka ƙwace daga wurinsa

"domin bawan Abimelek ya karbawa Ibrahim rijiyarsa"

Ban ji al'amarin ba sai yau

"Yau ne farkon da nake ji game da wannan"

Ibrahim ya ɗauki tumaki da shanu ya ba Abimelek

Wannan alamar alkawarin abokantaka ne da Ibrahim ya yarda ya yi da Abimelek. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-symaction)

Genesis 21:28

Ibrahim ya ware raguna bakwai na garken da kansu

"Ibrahim ya cire raguna guda bakwai daga garken"

Mene ne ma'anar waɗannan matan tumakin da ka shirya su da kansu?

"Me ya sa ka ware waɗannan raguna bakwan daga tumakin?"

za ka karɓa

"za ka ɗauke"

daga hannuna

Anan "hannu" na nufin Ibrahim ne. AT: "daga wuri na" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche)

domin su zama sheda domina

Ana iya sa wannan kalmar "sheda" a matsayin "tabbaci." AT: "domin tabbaci a gaban kowa da kowa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Genesis 21:31

Sai ya kira wacan wurin

"Ibrahim ya kira wacan wurin"

Biyasheba

Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa "ma'anar Biyasheba na iya zama "rijiyar alkawari" ko "rijiyar bakwai."

dukkan su

"Ibrahim da Abimelek"

Genesis 21:33

itacen sabara

Wannan itaciya ce wacce ba ta da ƙwari da za ta iya girma cikin hamada. Ana iya bayyana shi gaba ɗaya. AT: "wani itace" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)

Allah madawwami

"Allah rayaye har abada"

kwanaki ma su yawa

Wannan na nufi tsawon lokaci mai yawa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)