Genesis 20

Genesis 20:1

Shur

Wannan wani hamada ne gabashin iyakar yankin masar (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

ya aika mazajensa su ka ɗauko Sarai

"ya sa mazajensa su je su kawo masa Sarai"

Amma Allah ya zo wurin Abimelek

"Allah ya bayyana a wurin Abimelek

Duba

kalmar "duba" na kara jadada game da abin da zai biyo baya. "Saurare ni" (UDB)

kai mataccen mutum ne

Wannan wani mumunar hanya ce na cewa sarkin zai mutu. AT: "lalle ne ka kusan mutuwa" ko "Za ɗauke ran ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

matar mutum

"matar aure ce"

Genesis 20:4

Yanzu ... ce

Ana amfani da wannan kalmar wajen sa alamar canja labari zuwa bayani game da Abimelek. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#writing-background)

Abimelek kuma bai kusance ta ba

Wannan wani hanyar cewa ne bai yi jima'i da ita ba. AT: "Abimelek bai kwana da Sarai ba" ko "Abimelek bai taba Sarai ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

har ma al'umma mai adalci

"al'umma" a nan na nufi mutanen ne. Abimelek ya damu cewa ba shine kadai Allah zai hukunta ba, har da mutanen sa. AT: "har ma da mutanen da basu da laifi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

ba shi da kansa ne ya ce da ni 'ita 'yar'uwataba ce?' Har ma ita da kanta ta faɗa, cewa 'Shi ɗan'uwana ne'

Wannan yana da ambato cikin zance. Ana iya bayyana su azaman maganganun kai tsaye. AT: "ba shi da kansa ne ya ce da ni wai 'ita 'yar'uwarsa ba ce? Har ita ma kanta ta ce shi ɗan'uwanta ne" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

Na yi wannan bisa nagartar zuciyata, da kuma rashin laifofin hannuwana

Anan "zuciya" na nufin tunaninsa ko ƙudurisa. "hannu" kuma na nufi abun da ya aikata. AT: "Na aikata wannan da nufin mai kyau" ko "Na yi wannan ba tare da nufin aikata mugunta ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 20:6

Allah y ce da shi

"Allah ya ce da Abimelek"

ka taɓa ta

Wannan maganar na nufi yin jima'i da Sarai. AT: "ka kwana da ita" ( Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

matar mutumin

"matar Ibrahim"

za ka rayu

"Zan bar ka ka rayu"

dukkan wanda ke naka

"dukkan mutanen ka"

Genesis 20:8

Ya faɗa musu duk waɗanna abubuwa

"Ya faɗa musu dukka abubuwan da Allah yace da shi"

Me kenan ka yi mana?

Abimelek na amfani da tambaya ya tuhume Ibrahim. AT: "Ka aikata mana mumunar abu!" ko "Duba abin da ka yi mana!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Yaya na yi maka laifi, da ka jawo ... zunubi?

Abimelek na amfani da tambaya ya tunashe Ibrahim cewa bai yi masa zunubi ba. AT: "Ban yi maka laifin komai ba da har za ka kawo ... zunubi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

a ka jawo wa mulkina da ni kaina wannan babban zunubi

Ana maganar sa mutum ya aikata laifi kamar wani abu ne da ake iya ɗaura wa wani a kai. AT: "da zaka ɗaura wa ni da mulkina aikata irin wannan mumunar zunubi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

a bisa mulkina

"mulki" a nan na nufi mutane ne. AT: "a bisa mutanen da nake mulki" ( Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba

"Bai kamata ka yi mini haka ba"

Genesis 20:10

Me yasa ka yi wannan abin?

"Me yasa ka yin wannan?" ko "Me dalilin da yasa ka aikata wannan?" Ana iya ba da gamsashen bayanin abin da Ibrahim ya aikata. AT: "Me yasa ka ce da ni Sarai 'yar'uwarka ce?" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Ibarahim yace , 'domin na yi tsammanin cewa hakika babu tsoron Allah a wannan wurin, kuma za su kashe ni sabo da matata.'

AT: "Domin na ni tunanin cewa babu wani mai tsoron Allah a nan, wani na iya kashe ni domin ya ɗauki mata ta." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes and /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

babu tsoron Allah a wannan wurin

Anan "wuri" yana nufin mutane. AT: "babu wani a nan Gerar da ke tsoron Allah" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Bayan haka kuma hakika ita 'yar'uwata ce

"Amma da gaske ma Sarai 'yar'uwata ce" ko "har ila yau, lalle Sarai 'yar'uwata ce"

'yar mahaifina ce, amma ba 'yar mahaifiyata ba

"Mahaifin ɗaya ne, amma mahaifiyar dabam ne"

Genesis 20:13

Muhimmin Bayani:

A aya 13 Ibrahim ya ci gaba da ba Abimelek amsa.

gidan mahaifina

Anan "gidan" na nufin iyalin Ibrahim. AT: "mahaifina da sauran iyali na" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Na ce da ita dole ne ki nuna mini wannan aminci a matsayin matata: A duk inda mu ka je mu ka je ki faɗi haka game da ni, "Shi ɗan'uwana ne.""

AT: "Na ce da Sarai, ina so duk inda muka je ta nuna min aminci wajen faɗin cewa ni ɗan'uwanta ne" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotesinquotes da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-quotations)

Abimelek ya kwashi

"Abimelek ya kawo wasu" (UDB)

Genesis 20:15

Abimelek yace

"Abimelek ya cewa Ibrahim"

ƙasar tawa tana gabanka

Wannan wani hanyar cewa "Ina mika dukka ƙasa tawa a gare ka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Ka zauna a duk inda ya yi maka kyau

"Yi zama a inda ka ke so"

dubu

"1, 000" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-numbers)

domin ya shafe duk wani laifi da na yi muku ne a fuskarku dukka, da kuma a gaban kowa da kowa

Ana maganar bayar da kudi domin nuna cewa ba ta da laifi kamar wani marufi ne da aka rufe laifi domin ka da kowa ya gani. AT: "Ina ba shi wannan, domin duk waɗanda su ke tare su san cewa ba ka aikata wani laifi ba" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

gaban kowa da kowa, hakika kun yi abin da ke dai-dai

Ana iya bayana "yin abin da ke dai-dai" ta wani hanya. AT: "kowa da kowa zai san cewa ba ka da laifi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 20:17

marasa haihuwa baki ɗaya

"ba za su iya samun 'ya'ya ba baki ɗaya"

Saboda Sarai matar Ibrahim

Ana iya ba da gamsashen bayani haka. AT: "domin Abimelek ya ɗauki matar Ibrahim Sarai" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)