Genesis 19

Genesis 19:1

Mala'ikun guda biyu

A Farawa 18 an bayana cewa mutane biyu sun tafi Spdom. A nan a bayana mana cewa mala'iku ne. (Duba: Farawa 18:22)

a ƙofar Ssodom

"hanyar shigar birnin Saduma." Akwai ganuwa kewaye da birnin, lalle ne mutane su bi ta ƙofar kafin su shiga. Wannan muhimmin wurin ne a birni. Muhimman mutane ne suke zama a wurin.

sunkuyar da fuskarsa har ƙasa

Ya sa gwiywar sa a ƙasa, sai goshinsa da hancinsa kuma na ƙasa.

shugabannina

Wannan kalmar bangirma ne da Lot ya ba wa mala'ikun.

Ina roƙon ku da ku biyo ta gidan baranku

"Na roƙe ku, ku tsaya a gidan bawanku"

wanke ƙafafunku

Mutanen na son wanke ƙafafunsu bayan tafiya.

zamu je mu kwana

Lokacin da mala'ikun suna magana, suna magana game da su biyu ne ba tare da Lutu ba. Su biyun sun shirya su kwana a kwararo. Wasu harsuna na iya amfani da "mu" a nan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)

Kwararo

Wannan a nufi filin gari ne, na jama'a.

su ka tafi tare da shi,

"suka juya su tafi tare da shi"

Genesis 19:4

kafin su kwanta

"kafin mutanen gidan Lot su kwanta su yi barci"

mazajen birnin, mazajen Sodom

"mazajen birni, wato, mazajen Sodom" ko kuma "mazajen birnin Sodom"

da tsofaffinsu da matasansu

"daga kananan matasan zuwa tsofaffi." Ma'anar wannan shine "mazaje na kowa ne shekara" na Sodom, suka kuma kewaye gidan Lot.

da suka zo a gare ka

"wancan ya shiga gidan ka

domin mu kwana da su

"mu yi jima'i da su." Mai yiwuwa harshenku na wata hanyar faɗin wannan cikin da'a. AT: "mu san su ta wurin kwana da su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism)

Genesis 19:6

bayansa

"bayan ya fita" ko "bayan ya wuce"

kada ku yi aikin mugunta irin wannan

"kada ku aikata wani mummunan abu haka" ko "kar kuyi irin wannan mummunan abu"

duk abin da yi kyau a gare ku

"duk abinda kuke so" ko "duk abinda kuke tunani dai-dai ne"

suna nan ne a ƙarƙashin rufana

Mutane biyun baƙi a gidan Lot, kuma lalle ne ya kare su. Kalmar "rufa" na matsayin gidan Lot ne, da kuma tsare su da Lutu zai yi. AT: "a cikin gida na, kuma Allah ya bukace ni in kare su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-synecdoche da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

Genesis 19:9

Ka tsaya can!

"ma sa gefe!" ko "tashi mana a hanya!" (UDB)

Shi da ya zo baƙunta

"Wannan da ya zo daga waje" ko "Wannan baƙon da ya zo zama a nan"

Wannan

"Lot." Mutane na magana a tsakanin su. Idan wannan magana ba a fili ya ke ba a harshenku, kuna iya ambata cewa mutanen na magana game da Lot ne a nan, kamar a UDB.

kuma ya zama alƙalinmu

"yanzu yana tunani cewa ya na da yanci ya gaya mana abin da ke daidai da wanda ba dai-dai ba" ko "ba za mu yarda masa ya zo ya hana mu aikata abin da mu ke so ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Yanzu shi

"kuma ba shi wani dalili mai kyau na yin haka, shi" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Yanzu, mu

"Domin ka na gaya mana cewa abin da mu ke yi ba daidai ba, mu"

zamu ci mutuncika fiye da yadda zamu yi musu

Mazan sun yi fushi da Lot domin ya ce, "kada ku aikata wannan muguntar" (Farawa 19:6), to yanzu suna yi ma sa barazana cewa za su aikata muguntar fiye da yadda ya ke tunani a farko. AT: "za mu aikata mugunta a gare ka fiye da yadda zamu yi musu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Suka matsa wa Lutu, suka zo kusa da ƙofar domin su ɓarke ta

Ma'ana mai yiwuwa shi ne 1) "suka ci gaba da zuwa kurkusa da mutumin, wato Lot, har sun kai kusa da inda za su iya ɓarke kofar" ko 2) suka ture Lot zuwa bango, ko ƙofar gidan, suna shirin ɓarke ƙofar.

Genesis 19:10

Amma sai mutanen

"Amma bãƙi biyun na gidan Lot" ko "Amma mala'iku biyun"

mutanen suka miƙa hannuwansu suka shigo ... ciki suka kulle

Harshenku na iya bukaci a ambata cewa mutanen sun buɗe kofar tukunna. AT: "mutanen suka buɗe kofar domin su iya mika hannayensu su jawo... su, sai suka kulle" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Sai bãƙin na Lot suka bugi mutanen da makanta

Kalmar "bugi da makanta" ba ya nufi cewa bãƙin sun dau hannu ko wanni abu suka bugi mutanen kamar yadda muka gane kalmar "bugi" ba. AT: "bãƙin na Lutu suka makantar da mutanen" ko "sun hana su iya gani" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

duk da matasan da tsofaffin

"mutane na kowani shekara." Wannan na jadada cewa bãkin sun makantar the dukka mazan. Wannan na iya nuna matsayin mutum maimakon shekaru. AT: "da manya da kanana" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)

Genesis 19:12

Sai mutanen suka ce

"Sai mutane biyun suka ce" ko "Sai mala'iku suka ce"

Ko kana da wani naka a nan?

"Akwai wani da ke na gidanka kuma a cikin birnin?" ko "Kana da wani ɗan iyalinka a wannan wurin?"

duk wanda ka ke da shi a cikin birnin

"wani daga iyalinka da ke zama a birnin"

mu na gab da hallakar

Wannan kalmar "mu" na nufin mala'ikun ne su biyu kadai zasu hallakar da birnin, ba tare da Lot ba. Idan harshenku na da yadda za a iya bayana haka, to a yi amfani da shi a nan. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-exclusive)

zargin da ake yi wa birnin a gaban Yahweh ya yi yawa

Ana iya canja kalmomin nan ta wani hanya domin a bayana kalmar "zargi." AT: "mutane da yawa sun kawo kuka cewa mutanen birnin nan na aikata mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns) da kuma yadda aka fassara waɗannan kalmomin a Farawa 18:20

Genesis 19:14

Sai Lot ya tafi

"Don haka Lot ya bar gidan"

da surukansa, wato mazajen da suka yi alƙawari za su auri 'ya'yansa mata

Kalmomin "mazajen da suka yi alkawarin aure 'ya'yansa mata" na bayana kalmar "surukai" ne. AT: "mazajen da za su aure 'ya'yansa mata" ko "samaran 'ya'yansa mata" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)

Da safiya ta yi

"kafin tashiwan rana"

Ka fito

"tashi yanzu"

kada a share ku tare a cikin wannan hukunci na birni

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "domin kada Yahweh ya hallakar da kai sa'ad da yana hukunta mutanen wannan birnin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

na birnin

"Birnin" a nan na nufin mutanen ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

Genesis 19:16

Amma ya yi jinkiri

"Amma Lot ya ɗan dakata" ko "Amma Lot ba ya fara tafiya"

Sai mazajen suka kama

"sai mazaje biyun suka kama" ko "sai mala'iku suka kama"

ya yi masa jinƙai

ya ji tausayin Lot." Ana bayana Yahweh a matsayin "mai jinƙai" domin ya kare Lot da iyalinsa ba tare da hallakar da su ba tare da mutanen Sodom ba.

Da suka fitar da su waje

"Sa'ad da da maza biyun suka fitar da Lot da iyalinsa waje"

Ku tserar da rayukanku!

Wannan wani hanyar faɗa masu cewa su tafi a guje domin kar su mutu. AT: "ku tafi a guje domin ceton rayuwanku!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

Kada ku waiga baya

A fahimci cewa ana magana game da birnin ne. AT: "Kada ku juya baya ku dubi birnin" ko "Kada ku juya baya ga Sodom" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis)

a wannan filin

Wannan na nufin filin wajajen Kogin Yodan.

domin kada a share ku

A fahimci cewa za a share su da mutanen birnin. AT: "ko Allah ya hallakar da ku tare da mutanen birnin" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-ellipsis da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 19:18

Baranku ya sami tagomashi a wurinku

Ana magana game da "gamshe" wani kamar 'tagomashi" wani abu ne da ake iya samuwa."a wurinku" kuma na wakilce tunani ko ra'ayi mutum. AT: "Kun sami gamsuwa a gare ni" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

kun nuna mini kirki sosai da ku ka ceci raina

AT: "kun yi mini kirki sosai ta wurin ceton raina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Ba zan iya kai wa kan duwatsu ba, masifar za ta same ni, kuma zan mutu

Ana maganar yadda Lot ba zai iya barin Sodom ba kafin Allah ya hallakar da birnin kamar "masifar" wani mutum ne da zai bi Lot a guje har ya kama shi. AT: "Lalle ne ni da iyalina mu mutu idan Allah na hallakar da mutanen Sodom domin duwatsun na da nisa, ba za su iya kai wurin ba a cikin lafiya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)

bari in je can domin tsira

Ana iya ba da gamsashen bayani game da roƙon Lot a haka. AT: "maimakon hallakar da wancan birnin, bari in gudu zuwa wurin domin tsira" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

rayuwata za ta cetu

Wannan na nufin cewa Lot da iyalinsa za su cetu. AT: "domin in kasance a raye" ko "domin in rayu" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 19:21

Na biya maka wannan buƙatan

"Zan yi abin da ka tambaya"

ba zan yi wani abu ba

Ana iya ba da gamsashen bayani wannan. AT: "ba zan hallakar da sauran biranen ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Zowar

Masu juya wannan na iya sharihinta cewa "sunan Zowar na kamar kalmar da ke nufi 'ƙarami' a Ibraniyanci. Lutu ya kira wannan garin 'ƙarami' a Farawa 19:20."

Genesis 19:23

Rana ta ɗaga bisa duniya

"Rana ta tashi bisa duniya." Ana iya barin wannan maganar "bisa duniya" ba tare wani bayani ba kamar yadda ya ke a UDB. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

a lokacin da Lot ya isa Zowar

An nuna cewa dangin Lutu suna tare da shi. AT: "lokacin da Lutu da iyalinsa suka isa Zowar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

Sai Yahweh ya saukar da ruwan wuta da matsanancin zafi bisa Sodom da Gomora

Jimlar "daga Yahweh" na nuna ikon Allah wajen sa farar wuta da wuta mai zafi su sauko a birnin. AT: "Yahweh ya sa farar wuta da kuma wuta mai zafi su sauko da sama a Sodom da Gomora" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

farar wuta da wuta mai zafi

Ana amfani da waɗannan kalmomin guda biyu tare don bayyana abu ɗaya. AT: "konewar sulfur" ko "ruwan sama mai zafi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-hendiadys)

waɗancan biranen

Wannan na nufi Sodom da Gomora ne musamman, amma kuma da wasu garuruwa guda uku.

da mazauna biranen

"mutanen da suke zama a biranen"

Genesis 19:26

ta zama al'amudin gishiri

"ta zama gunkin gishiri" ko "gikin ta ya zama kamar dutsen gishiri." Domin ta yi wa mala'ikan rashin biyayya wajen juya baya, Allah ya sa ta zama wani abu kamar gunki da aka yi da gishiri.

Duba

Kalmar nan "duba" na jawo hankali ga maganar mai ban mamaki da ke zuwa.

kamar na hayaƙin wutar makera

Wannan na nuna cewa hayaƙin na da yawa. AT: "kamar hayaƙi daga babban wuta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-simile)

Genesis 19:29

Muhimmin Bayani:

Aya 29 ya taƙaita wannan sura.

Allah ya tuna da Ibrahim

Wannan na bayana dalilin da ya sa Allah ya ceci Lot. Wannan bai nuna cewa Allah ya manta da Ibrahim ba ne a baya, amma ya dubi Ibrahim ya kuma nuna masa jinƙai. AT: "Allah yayi tunani game da Ibrahim sai ya kuma nuna masa jinƙai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

daga wannan hallakarwar

"daga hallakar" ko "daga hatsari"

Genesis 19:30

Lot ya fita daga Zowar zuwa duwatsu

An yi amfani da maganar cewa "fita daga" domin Lot ya tafi inda yake da tudu a duwatsun ne.

Genesis 19:31

Babbar 'yar

"'yar farin Lot" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-nominaladj)

ƙaramar

"ƙaramar 'yar" ko "kanwar ta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-nominaladj)

bisa ga tsarin dukkan duniya

"Duniya" a nan na nufi mutanen ne. AT: "kamar yadda mutane ke yi a koina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metonymy)

sha ruwan inabi

Ana iya ba da gamsashen bayani cewa manufar su shine su sa shi ya bugu. AT: "sha ruwan inabi har sai ya bugu" (UDB) ko "ya bugu da ruwan inabi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

domin mu wanzar da sunan mahaifinmu

Wannan na maganar ba wa Lot zuriya kamar iyalinsa na jere ne kuma ana ƙokarin kara tsayi. AT: "domin mu iya haifar da 'ya'ya da za su zama zuriyar mahaifinmu" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

bai ma san lokacin da ta kwanta ba , bai kuma san lokacin da tashi ba

"bai san komai da ya faru ba" ko "bai ma san cewa ta kwanta da shi ba"

Genesis 19:34

sai mu sa shi ya sake buguwa da ruwan inabi ... ko lokacin da ta tashi ba.

A fassara waɗannan kalmomi kamar yadda aka yi a Farawa 19:31.

sha ruwan inabi

Ana iya ba da gamsashen bayani cewa manufar su shine su sa shi ya bugu. AT: "sha ruwan inabi har sai ya bugu" (UDB) ko "ya bugu da ruwan inabi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-explicit)

domin mu wanzar da sunan mahaifinmu

Wannan na maganar ba wa Lot zuriya kamar iyalinsa na jere ne kuma ana ƙokarin kara tsayi. AT: "domin mu iya haifar da 'ya'ya da za su zama zuriyar mahaifinmu" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

bai ma san lokacin da ta kwanta ba , bai kuma san lokacin da tashi ba

"bai san komai da ya faru ba" ko "bai ma san cewa ta kwanta da shi ba"

Genesis 19:36

suka yi junabiyu ta wurin mahaifinsu

"suka ɗauki ciki ta wurin mahaifinsu"

Ya zama

"Shi ne"

Mowobawa a yau

"mutanen Mowab da suke a raye yanzu"

a yau

Kalmar "a yau" na nufin lokacin da marubicin littafin Farawa na a raye ne. An haifi marubucin wannan littafi da lokacin da yayi wannan rubutu shekaru da yawa ne bayan rayuwar Lot da iyalinsa sun mutu.

Ben Ammi

Wannan sunan namiji ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

mutanen Ammon

"zuriyar Ammon"