Genesis 18

Genesis 18:1

Mamre

Wannan sunan mutumin mai itacen rimi..

a ƙofar rumfa

"a ƙofar rumfar ko alfarwa"

tsakar rana

"zafin rana"

Ya duba sama, sai ga mutane uku na tsaye

"Ya duba sama, sai ga mutane uku suna tsaye"

kewaye da shi

"kur kusa" ko "wurin." suna kusa da shi, amma da dan nisa da zai iya gudu zuwa wurin sa.

sunkuya ƙasa

Wannan na nufi nuna ban girma da tawali'u, da kuma daraja wani.

Genesis 18:3

Ubangiji

Wannan laƙani ne na ban girma. Ma'ana mai yiwuwa sune 1) Ibrahim ya san cewa ɗaya daga cikin mutanen Allah ne, ko 2) Ibrahim ya san waɗannan mutanen wakilan Allah ne.

a wurin ka

Ibrahim na magana da wani a tsakanin mutanen. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

kada ka wuce

"kada ka ci gaba da tafiya"

bawanku

"ni." Ibrahim na nufin da kansa ne haka domin ya nuna ban girma wa bãƙonsa.

Bari a kawo ɗan ruwa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Bari in kawo muku ruwa" ko "Bari bawa na ya kawo muku ruwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

ɗan ruwa ... maku abinci

"ruwa ... abinci." Ambacin "ɗan" wata hanyar nuna karimci. Ibrahim za ba su ruwa da abinci fiye da abun da suke bukata.

wanke ƙafafu

Wannan al'ada ne na taimakon matafiya ne koren gajiya bayan tafiya mai nisa.

Genesis 18:6

awo uku na gãri

kamar lita 22 (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-bvolume)

Ya hanzarto

"bawan ya ruga guje"

gyara shi

"a yanka a kuma gasa shi"

soyen

Wannan sashin madara ne da ke daskare.

maraƙin da aka gyara

"maraƙin da aka gasa"

Genesis 18:9

Suka ce da shi

"Sa'annan suka ce da Ibrahim"

Ya ce hakika zan komo wurinka

Kalmar "Ya" na nufi da mutumin da Ibrahim ya kira shi "Ubangiji" a Farawa 18:3.

baɗi war haka

"idan wannan lokacin ya zo shekara ta gaba" ko "game da wannan lokacin shekara mai zuwa"

kuma duba

Kalmar "duba" na jan hankalin mu ne ga lura da bayani mai ban mamaki da ke zuwa.

Genesis 18:11

Bayan na tsufa, shugabana kuma ya tsufa, ko zan sami wannan jin daɗin?

Zai iya yiwuwa a kara cewa "jin daɗi na samin ɗa" (UDB). Sarai ta yi irin wannan tambaya domin ba ta gaskanta cewa za ta iya samun ɗa ba. AT: "Ba gaskanta cewa zan fuskance farincikin samun ɗa ba. Shugabana ma ya tsufa sosai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

shugabana ya tsufa

Ma'anar wannan shine "tunda yake miji na ma ya tsufa."

shugabana

Wannan laƙanin ban girma ne da Sarai ta ba wa mai gidan ta Ibrahim.

Genesis 18:13

"Me yasa Sarai ta yi dariya ta kuma ce, "Ko hakika zan iya haifar ɗa Yanzu da na tsufa"?

Allah yayi amfani da tambaya domin ya nuna wa Ibrahim cewa ya san abin da Sarai ke tunani a zuciyar ta, kuma baya ji dadi ba. Ha maimaita tambayar da Sarai ta yi a Farawa18:11 da wasu kalmomi dabam. AT: "Sarai ba ta yi daidai ba da yin dariya ta kuma ce, "ba zan iya haifar ɗa ba domin na tsufa sosai!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Ko akwai abin da ke da wuya ne ga Yahweh?

"Ko akwai abin da ba zai iya yi ba? Yahweh na magana game da kanshi kamar yana maganar wani ne, domin ya tunashi Ibrahim cewa, Shi, Yahweh, mai girma ne kuma zai iya yin komai. AT: "Ba abin da ni, Yahweh ba zan iya yi ba!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

A dai-dai lokacin dana sa, kamar war haka

"A lokacin da na zaba, kamar war haka"

Sai Sarai ta yi musu

"Sai Sarai ta yi musu ta na cewa"

Ya amsa

"Yahweh ya amsa"

A'a kin yi dariya

"I, kin yi dariya." Ma'anar wannan ita ce "A'a, ba gaskiya ba; haƙiƙa kin yi dariya."

Genesis 18:16

ya raka su a kan hanyarsu

"ya sa su a hanyarsu" ko " domin ya yi bankwana da su". Ya kasance mai ladabi a ɗan yi nisa tare da baƙi yayin da suke barin.

Ko zan ɓoye wa Ibrahim abin da zan aikata ... shi?

Allah yayi amfani da tambaya a nuna cewa zai yi wa Ibrahim magana game da wani muhimmin abu, kuma zai fi kyau ya yi haka. AT: "Bai kamata in ɓoye wa Ibrahim abin da na ke shirin yi ba, kuma ba zan ɓoye ba ... shi." ko " Ya kamata in faɗa wa Ibrahim abin da na ke shirin yi, kuma zan faɗa ma shi... shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

dukkan al'uman duniya za su sami albarka ta wurinsa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Zan albarkaci dukka al'uman duniya ta wurin Ibrahim" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

domin ya koya

"cewa zai shiryar" ko "don ya umarta"

su bi tafarkin Yahweh ... domin Yahweh ya cika ... da ya faɗa

Yahweh na magana game da kanshi kamar wani ne dabam. AT: "domin kiyaye abin da ni, Yahweh na ke so ... Ni, Yahweh, zan kawo ... na faɗa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

su aikata adalci da aikin adalci

Wannan na faɗin yadda za a kiyaye hanyar Yahweh.

domin Yahweh ya cika abin da ya faɗa wa Ibrahim zai aikata a gare shi

"domin Yahweh ya albarkace Ibrahim kamar yadda ya ce zai yi." Wannan na nufin alkawarin albarkar Ibrahim na mayar da shi babban al'uma.

Genesis 18:20

Saboda kukan Sodom da Gomora ya yi yawa

Ana iya juya waɗannan kalmomi domin a nuna cewa kalmar "kuka" na nufin "zargi" ne. AT: "Mutane dayawa na zargin 'yan Sodom da Gomora akan aikata mugayen abubuwa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

zunubinsu ya haɓaka

"sun aikata zunubi da yawa"

Yanzu zan sauka zuwa wurin

"Yanzu zan sauka zuwa Sodom da Gomara"

in ga kukan ... ya zo gare ni

Yahweh na magana kamar ta wurin zargin da ke zuwa daga mutanen da suka wahala ne ya san abin da yake faruwa. AT: "muguntar ya kai yadda mutanen da suke zargin su ke faɗi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-abstractnouns)

Genesis 18:22

juya daga can

"bar inda Ibrahim ya ke"

Ibrahim ya tsaya a gaban Yahweh

"Ibrahim suka tsaya tare da Yahweh"

matso

"matso wurin Yahweh"

share

Ibrahim na maganar hallakar da mutane kamar sharar da ake yi da tsin-tsiya. AT: "hallakar" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

adalai tare da mugaye

"adalan mutane tare da mugayen mutane"

Genesis 18:24

Muhimmin Bayani:

Ibrahim ya ci gaba da magana da Yahweh.

Ko za ka hallaka shi ba tare da la'akari da adalan nan hamsin ba da ke can?

Ibrahim na begen cewa Yahweh zai ce, "Ba zan hallakar da shi ba." AT: "I tsamanin ba za hallakar da shi ba, ta dalilin adalai hamsin da su ke can" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Ba zai yiwu ba ka yi haka

"Ba zan taba so ka yi abu irin wannan ba" ko "Bai kamata ka so aikata abu irin wannan ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

abu haka, wato ka kashe

"abu haka kamar kisa"

a hori adalai kamar yadda aka hori miyagu

Wannan za a iya bayyana a cikin aikatau. AT: "ka bi da adalai dai-dai da yadda za ka bi da mugaye" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Ba zai yiwu ba Mai Hukunta duniya ya yi abin da ke dai-dai?

Ibrahim ya yi amfani da tambaya domin ya bayana abin da ya ke tsamani Allah ya yi. AT: "Na tabbata Mai Hukuncin duniya zai yi adalci" ko "Tun da ya ke kai ne mai hukuta dukka duniya, tabas za ka yi abin da ke dai-dai!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)

Genesis 18:27

Duba

Kalmar "Duba" a nan na jawo hankalin mu ne ga maganar da ke zuwa a gaba.

Na jawo wa kaina magana

"Gafarce ni domin ƙarfin zuciyar da na ɗauka wajen managa da kai" or "Garfarce rashin tsoro na wajen yin magana"

da Ubangijina

Ibrahim na nuna bangirman da ya ke da shi ga Yahweh ta wurinmagana kamar yana yi da wani dabam. AT: "a gare ka, ya Ubangijina" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-123person)

ƙura ce kawai da toka

Wannan ƙarin magana ne da bayana Ibrahim a matsayin mutum da zai mutu ya kuma zama ƙura da toka. AT: "mutum kawai mai mutuwa" ko "marasa muhimminci kamar ƙura da toka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)

ba su kai hamsin ba da mutum biyar

"adalai arba'in da biyar kawai"

sabo da rashin mutum biyar

"in ya ka sa da adalai mutum biyar"

Genesis 18:29

Ya yi masa magana

"Ibrahim ya yi magana da Yahweh"

To a ce za sami arba'in a can

Ma'anar wannan shine "A ce ka sami adalai guda arba'in a Sodom da Gomora."

Ya amsa

"Yahweh ya amsa"

Saboda mutane arba'in ɗin ba zan yi ba

"Ba zan hallakar da biranen ba, in na sami adalai mutum arba'in a can"

talatin

"adalai mutum talatin" ko "mutanen kirki guda talatin"

Na jawo wa kaina magana

"Gafarce ni domin ƙarfin zuciyar da na ɗauka wajen managa da kai" or "Garfarce rashin tsoro na wajen yin magana"

ashirin

"adalai mutum ashirin" ko "mutanen kirki guda ashirin"

Genesis 18:32

Wataƙila za a sami goma a can

"Wataƙila fa ka sami adalai mutum goma a can"

goma

"adalai mutum goma" ko "mutanen kirki guda goma"

Sai ya ce

"Sai Yahweh ya amsa"

saboda mutane goman

"Idan na sami mutane goma adalai a can"

Sai Yahweh ya kama hanyarsa

"Yahweh tashi daga wurin" ko "Yahweh ya tafi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)