Ana amfani da wannan magana a nan domin ba da alama ce na sabon sashin labarin. Idan harshen ku na da wata hanya yin haka, to ana iya amfani da ita.
"Allah wanda ke da iko duka"
Tafiya na nufin rayuwa ne a nan, kuma "a gabana" na nufin biyayya. AT: "Yi rayuwar da na ke so" ko "Yi ma ni biyayya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-metaphor)
"Zan ba da alƙawarina" ko " Zan cika alƙawarina"
A wannan ne Allah ya yi alƙawarin albarkace Ibram, amma ya na bukatan Ibram ya yi biyayya a gare shi.
"zan ƙara yawan zuriyarka ƙwarai" ko "zan ba zuriya masu yawa ƙwarai" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"Ibram ya fadi, fuskarsa kuma a ƙasa" ko "Nan da nan Ibrahim ya sa furkarsa a ƙasa" .Ya yi haka ne domin ya nuna girmar da ya ba Allah, kuma zai yi masa biyayya.
Allah yayi amfani da wannan maganar domin ya gabatar da abin da zai yi wa Ibram daga na shi bangaren alƙawarinsa da Ibram.
Kalmar "duba" a nan na bayana tabbacin abun da zo nan gaba: "haƙika alƙawarina na tare kai."
"uban al'ummai masu yawa ƙwarai" ko "al'ummai da yawa zasu sami sunansu daga gare ka"
Masu fassarar wannan na iya sharihinta cewa, ma'anar sunan "Ibram" kuwa shi ne "uba mai daraga" sunan "Ibrahim" kuma na kamar "uban dangi masu yawa."
"Zan sa ka sami zuriya masu yawa"
"Zan sa zuriyarka su zama al'umma da yawa"
"daga cikin zuriyarka za a sami sarakuna" ko "wasu daga zuriyarka za su zama sarakuna"
Allah ya ci gaba da yi Ibrahim magana.
"na kowani tsara"
"a matsayin alkawari da zai kasance har abada"
"in zama Allahn ka da na zuriyarka"
Kan'ana, a matsayin mallakarka har abada" ko "Kan'ana, ka mallaka har abada"
Wannan maganar na gabatar da abin da Ibram ke bukatar yi a na shi matsayin a sashi alƙawarin shi da Allah.
"kula da alƙawarina" ko "yi biyayya da alƙawarina"
"Wannan ita ce sharaɗin alƙawarina." Wannan jimlar na gabatar da bangaren alƙawarin ne da dole Ibram ya kiyaye.
Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai aiki. 'Dole ne ka yi wa kowani na miji a cikinku kaciya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Wasu al'ummomin na iya son ƙaramin bayanin kwatanci kamar "Dole ne a yi muku kaciya." Idan fassarar ku ta "a kaciya" ta riga ta ƙunshi kalmar don "kaciyar fata", ba kwa buƙatar maimaita ta. Ana iya sanya wannan aiki. AT: "Dole ne ku yi wa kowane ɗa namiji kaciya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-euphemism da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"alamar da ke nuna cewa akwai alƙawarin"
Ma'ana mai yiwuwa 1) "alamar" ko 2) "wani alama." Na farko na nufin cewa iyakar alamar kenan gode ɗaya, na biyun kuma na nufi cewa alamar na iya kasance fiye da ɗaya. Kalmar "alama" a nan na ba da tuni ne na abin da Allah ya alƙawatar.
Allah ya ci gaba da yi wa Ibrahim magana.
"cikin kowani tsara"
Wannan na nufin bayi ne. AT: "kowani na miji da ka saya" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "za ka sa alamar alƙawarina a jikinka" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
"zama madawwamen alƙawari." Domin alamar a jiki ya ke, ba wani mai iya sharewa.
Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki, kuma kuna iya barin kalmomin da zasu ba da ma'ana mara kyau a yarenku. AT: "namijin da ba ka yi wa kaciya ba" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)
Ma'ana mai yiwuwa 1) "Zan yanke kowani namiji marasa kaciya ... daga mutanensa" ko 2) "Ina so ka yanke kowani namiji mara kaciya ... daga mutanensa"
"Baya kiyaye umurnin alƙawarina ba." Wannan ne dalilin da za a yanke shi daga mutanensa.
Kalmar "game da" in gabatar da mutumin da Allah ke magana a kai, da ke zuwa nan gaba.
"Zan sa ta haifar maka ɗa"
"za ta kasance kakar al'umai" (UDB) or "zuriyar ta za su zama al'ummai"
"Sarakunan mutane za su sauko daga gare ta." ko "Wasu zuriyar ta za su zama sarakunan mutane"
"a cikin tunanin sa" ko "ya ce da kansa a cikin zuciyarsa"
Ibrahim ya yi amfani da tambaya domin ya nuna rashin amincewa wai haka zai iya faruwa. AT: "haƙiƙa mutum mai shekara ɗari ba zai iya haifan ɗa ba!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion)
Ibrahim ya yi amfani da tambaya domin ya nuna rashin amincewa wai haka zai iya faruwa. Maganar "wadda ke shekara tasa'in" ya nuna dalilin da ya sa Ibrahim baya amince cewa Sarai za ta iya haifa ɗa ba. AT: "Shekaru Sarai tasa'an ne, za ta iya haifan ɗa?" ko "shekarar Sarai tasa'in ne, tabbas ne ba za ta iya haifan ɗa ba!" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-rquestion da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)
"Ina roƙo, bari Isma'ila ya gaji alƙawari da ka tsakani na da kai" ko "ko zai yiwu Isma'ila ya gaji alƙawarin albarkar ka." Ibrahim ya ba da sharawarar abin da tabbata zai iya faruwa.
Allah ya faɗa wannan domin ya canja wa Ibrahim tunaninsa na cewa Sarai baza ta iya samin ɗa ba.
Kalmar "ka" na nufi Ibrahim ne.
Wannan ƙarin magana ne da ke nufi "zan sa ya sami 'ya'ya dayawa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"shugabanni" ko "masu mulki." Waɗannan ubanne ba 'ya'ya goma sha biyu da jikokin Yakubu ba ne da zasu shugabanci kabila goma sha biyu na Isra'ila.
Allah ya koma ga maganar alƙawarin sa da Ibrahim, ya kuma jadada cewa da Ishaku ne zai cika alƙawarin ba Isma'ila ba.
"Da Allah ya gama magana da Ibrahim"
"Allah ya bar Ibrahim"
"kowani mutum namiji da ke gidan Ibrahim." Wannan na nufi dukka mutane maza na kowani shekara: jarirai, yara, da maza.
"Wannan ya kunshi waɗanda aka haifa a gidansa da kuma waɗanda ya saya a wurin bãƙi"
Wannan na nufi da bayi ne.